Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ghana Ta Bi Sawun Masu Taimakawa Najeriya


Shugaban Ghana, John Dramani Mahama.
Shugaban Ghana, John Dramani Mahama.

​Shugaban ECOWAS a halin yanzu, kuma shugaban kasar Ghana John Dramani Mahama, ya shiga sawun shugabanni masu neman taimakawa Najeriya saboda hakkin makwabtaka, da kuma matsayinsa na Shugaban ECOWAS a halin yanzu.

Mr. Mahama yayi alkawarin cewa zai yi iya bakin kokarinsa, wajen tabbatar da gani cewa an wargaza wannan kungiya da ake kira Boko Haram, saboda Najeriya ta samu zaman lafiya, kuma kasashen dake makwabtaka da ita suma su amfani daga zaman lafiyarta.

Shugaban na Ghana bai fito fili ya bayanna taka-mai-mai wani irin dauki zai kaiwa Najeriya ba, ko na dakarun Sojoji ne, ko kuma kayan aiki. Amma Asabar dinnan, wakilin Muryar Amurka a Ghana Baba Yakubu Makeri yayi kokarin jin ta bakin jami’an gwamnati akan irin wato irin tsarin da Ghana zata yi wajen taimaka wa Najeriya yaki da ‘yan ta’adda.

Amma jami’an gwamnati a Ghana sun bayanna cewa akwai taro da shuwagabannin hukumomin tsaro na kasashen dake karkashin kungiyar ECOWAS Talata mai zuwa, a birin Accra dake Ghana. Ana kyautata zaton a wajen taron ne za’a fito da tsari da kuma irin dabaru da za’a yi amfani dasu wajen yakar ‘yan bindigan da suka addabi jama’ar arewacin Najeriya.
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:13 0:00
Shiga Kai Tsaye
Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG