Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Babu Kawancen Kasuwanci da Tarayyar Kasashen Turai


Shugaban Kasar Ghana John Dramani Mahama.
Shugaban Kasar Ghana John Dramani Mahama.

Kungiyar Kwadagon kasar Ghana ta ja kunnen gwamnatin kasar kada ta kuskura ta sanya hannu akan yarjejeniyar kasuwanci da kungiyar tarayyar kasashen turai ba tare da yin la'akari da irin illar da yin hakan ka jawowa 'yan kasar

Kungiyar kwadago ta kasar Ghana tace kada gwamnatin kasar ta sa hannu a yarjejeniyar kasuwanci da kungiyar tarayyar turai ba tare da yin la'akari da yin hakan zai shafi 'yan kasar ba.

Jiya kungiyar tayi taron tattaunawa da 'ya'yanta akan mataki na gaba da kungiyar zata dauka idan gwamnatin kasar ta kuskura ta sanya hannu akan yarjejeniyar kulla kawancen kasuwanci da kungiyar tarayyar kasashen turai ba tare da neman shawararsu ba.

Tuni ita kungiyar kwadagon da wasu kungiyoyin jama'a kamar ta Kirista da ta kasuwanci da sauransu suka gabatarda karafinsu ga shugaban kasar John Dramani Mahama da yayi la'akari da irin mummunan tasiri da irn yarjejeniyar zata yi akan 'yan kasar Ghana.

Majalisar dokokin tarayyar Turai ta ba kasashen yammacin Afirka wa'adi har zuwa farkon watan Oktoba na shekara 2014 su sanya hannu domin su tabbatar da yarjejeniyar.

Bayan taron 'yan kwadagon shugaban tarayyar masana'antu masu zaman kansu na Ghana wanda ya halarci taron Nana Osebo cewa yayi ba wai sun ki yarjejeniyar ba ne amma a zamansu na kasa mai cin gashin kanta suna son su tsayar da matsaya daya kana su tuntubi kungiyar tattalin arzikin kasashen yammacin Afirka domin su tattauna kada a yi masu shigo-shigo ba zurfi. Yace kawo yanzu mutanensu 'yan kasuwa basu da cikakkiyar masaniya akan yarjejeniyar.

Shugaban masana'antun Ghana masu zaman kansu yace wajibi ne su yi muhawara akan yarjejeniyar su san abubuwan da ta kunsa. Yakamata su samu cikakkiyar fahimta domin su san illar dake cikinta, idan har akwai illa. Ba daidai ba ne a barsu cikin duhu.

Ministan cinikayya da manyan masana'antun kasar ta Ghana Haruna Idrisu yace dole ne Ghana ta bada kai bori ya hau. Yace bayan daya ga watan Oktoba na wannan shekarar idan Ghana bata sa hannu a yarjejeniyar ba zata fuskanci kasadar rashin samun shiga kasuwar Turai. Wannan yarjejeniyar itace ta maye gurbin ta Kwatano wadda aka yi shekarar 2008 tsakanin kasashen yammacin Afirka da Taurai. Saidai ministan yace akwai kokarin da gwamnati ta keyi ta rage dogaro akan kasuwar Turai. Yace a karo na farko kasar zata bude kasuwanci da kasashen China da Japan da Turkiya da Afirka Ta Kudu domin bunkasa kasuwanci da saka jari.

Gwamnatin tayi alkawarin fito da matsayin da zata dauka nan gaba.
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:06 0:00
Shiga Kai Tsaye
XS
SM
MD
LG