Kasashen duniya da dama sun yi alkawarin agazawa Najeriya da abubuwan da suka shafi harkokin tsaro domin a gano yaran. Kasashe kamar su Amurka da Ingila da Canada da Faransa sun ce a shirye suke su bada taimako tare da inganta matakan tasro a duk fadin kasar.
Shugaban Amurka Barack Obama yace Najeriya ta amince da tayin taimakon da suka yi. Da yake jawabi Firayim Ministan Ingila David Cameron yace yana son a gane cewa matsalar bata shafi Najeriya kadai ba. Matsala ce da ta shafi duniya gaba daya domin akwai wasu masu kaifin ra'ayin addini da suke neman su addabi jama'ar duniya. Yace wajibi ne su taimaka su fataktakesu domin a samu zaman lafiya a duniya baki daya.
Shi ma shugaban kasar Faransa cewa yayi babu shakka abun da ya faru kalubale ga duk shugaban kwarai kuma ya kamata ya taimaka.
To saidai tayin taimakon ya fara tayarda cecekuce a Najeriya. Yayin da wasu ke cewa kasar na cikin halin bukatar taimako wasu kuma cewa su keyi kasar bata bukatar wani taimako domin yaki da masu tada kayar baya musamman da yake lamarin na cikin gida ne. Wadanda suka ce bata bukatar taimako sun ce ina jami'an tsaron kasar suke wadanda suka taka rawar gani a wasu kasashen yammacin Afirka har sai da aka samu zaman lafiya a kasashen, irinsu Liberia da Saliyo da Mali. Sun kuma tambaya shin kudaden da aka kashe kuma ana cigaba da kashewa sun tafi banza ke nan. Sun cigaba da cewa sojojin Najeriya basu da wani anfani ke nan wato kowane dan Najeriya bashi da tsaro ke nan sai yayi ta kansa.
Wani abun lura kuma shi ne idan kasashen waje sun shiga wata kasa domin su yi taimako na 'yan kwanaki sai su kwashi shekara da shekaru basu bar kasashen ba. Kamata yayi Najeriya tayi la'akari da wannan.
Dr Abdullahi Wase wani masanin harkokin tsaro yace hakan ta faru a Afghanistan kuma daga karshe dole aka shirya sasantawa da 'yan Taliban. Amma muddin kasashen waje suka yi abun da suka ce zasu yi suka kuma kwashe nasuinasu suka fita komi ya yi daidai.
Ga karin bayani.