Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Yakamata Shugabannin Afirka Su Yi Koyi da Mandela


Wasu shugabannin Afirka
Wasu shugabannin Afirka

A firar da ya yi da abokiyar aiki Grace Abdu, Farfasa Boube Namaiwa ya ce kamata ya yi shugabannin Afirka su yi koyi da Mandela.

Akwai halayen kwarai na Nelson Mandela da yakamata shugabannin Afirka su yi koyi da su.

Farfasa Boube Namaiwa ya ce lokacin da aka sako Mandela daga kurkuku bayan ya kwashe shekaru ashirin da bakwai a tsare to da ko ya nemi yadda zai rama abun da aka yi masa kamar yadda ake gani a wasu kasashen Afirka yau. Amma ko da ya zama shugaban kasar Afirka Ta Kudu domin son kasarsa ta zauna lafiya mutanesa kuma su cigaba ya ce ya yafewa duk wadanda suka gana masa ukuba. Yau idan za'a iya samun irin hakan a kasashen Najeriya da Kamaru da Niger da ma wasu da an samu cigaba fiye da yadda ake yanzu. Ko a kasar Sudan da wasu idan da shugabannin zasu sa zamantakewa gaba to da ko ba'a samu wata matsala ba.

Ya ce a lura da abunbuwan dake faruwa a arewa maso gabashin kasar Najeriya inda kungiyar Boko Haram take saka bom a mijami'u domin suna kirista a kashesu alhali kuwa babu wanda zai ce shi kadai yake kan hanyar gaskiya sai dai mutum ya dubi abun da aka rubuta cikin littafi domin kowa tsammani ne yake yi. To sai dai a duba irin misalin da Nelson Mandela ya nuna mana na zaman lafiya. Domin a lokacin da ya zama shugaban kasa yana da wuka da nama a hannunsa da ya ce zai musgunawa fararen fata kamar yadda suka musguna masa to da yanzu babu zaman lafiya a Afirka Ta Kudu. Sabili da matakin da Nelson Mandela ya dauka yau gashi kasar tana cikin kasashe masu yunkurowa kamar su India da Brazil da Ghana da kasar Rasha. Yau zaman lafiya ya kankama a kasar har ma mutanen kasashe kamar su Zimbabwe da Mozambique da ma wasu suna zuwa neman aiki a kasar. Inda ba domin Mandela ya yafe ma mutanen da suka saba masa ba da babu zaman lafiya yau.

Kasar Afirka Ta Kudu tana da arziki kuma suna cin gajiyar arzikinsu. To amma a kasashe kamar su Mali da Ivory Coast inda aka yi yaki domin neman iko da Chadi ana kashe juna domin ko wasu sun rike iko ko kuma wasu suna neman iko. Mutane suna neman iko su zauna din-din-din iyakacin ransu. Sabili ke nan mutane su kan yi yaki su kashe juna. Amma a Afirka Ta Kudu ba'a yi haka ba domin dattakun Nelson Mandela da yau Afirka ta rasa gaba daya.

Ga karin bayani.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:04 0:00
Shiga Kai Tsaye
Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG