An rufe harabar da masu zanga-zanga ke cigaba da kira a nemo dalibannan, Alhamis dinnan a ranar da babban birnin kasar ke saukar bakin Taron Tattalin Arziki na Duniya akan Afirka.
An rufe birnin ruf, a dai-dai lokacin da take karbar bakoncin babban taro wanda aka tsara shi domin nuna albarkar kasuwanci a kasar da tafi kowace kasa tattalin arziki a Afirka.
Sai batun sace daliban ne ya mamaye tattaunawar taron Alhamis dinnan, a lokacin da Shugaba Jonathan ya bude taron da alkawarin nemo wadannan dalibai.
Jonathan ya godewa kasashen ketare kamar Amurka da Britaniya, da Faransa da Chana saboda irin gudumuwa da suka gabatar domin yunkurin nemo daliban, wadanda aka sace daga makarantarsu ta Sakandare dake Cibok ran 14 ga watan Afrilu.
Ya godewa wakilan da suka hallarci taron, duk da barazanar da mayakan sa kai suke dashi, kana ya hanzarta fara yin jawabi akan samar da ayyuka a tattalin arzikin kasashen Afirka.
Duk da alkawari da yayi, Jonathan ya amince akan gidan Talabijin a wannan mako cewa bashi da tabbacin inda daliban suke.