Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Buhari Yayi Sanarwa Akan Cibok


A dai-dai wannan lokaci da shuwagabannin duniya suke kawowa Najeriya dauki, wajen gani an nemo daliban Cibok mata wadanda aka sace su kusan 300 a makarantarsu ta Sakandare, dan siyasa, tsohon shugaban kasa kuma daya daga cikin shuwagabannin jam'iyyar APC Janar Muhammadu Buhari mai ritaya ya fitar da sanarwa.

Sanarwar mai dauke da sa hannun Mr. Buhari, an rubuta ta ne da turanci, kuma fassararta.

Daga Janar Muhammadu Buhari

"A makonnin da suka wuce, sace dalibai mata da akayi a Cibok, Jihar Borno ya nuna a fili irin barazanar da muka dade muna fama dashi a kasarnan, daga ayyukan mutanen da basu fahimci Musulunci ba.

Addu’o’in mu suna tare da iyalen wadanda suka rasa ‘yan uwansu a wannan tashe-tashen hankula da muke ta gani. Sannan kuma muna mika alhininmu ga iyayen da ‘ya’yansu suke cikin hannun wadannan mugayen mutane.

Wannan mummunan bidiyo da aka saka a yanar gizo, ya nuna a fili cewa shaidanun mutanennan basu da zuciya. Ya nuna ko suwaye su a fili, kuma maza kamar wadanda bai kamata a ce suna keta diyaucin kasa ba. Daga abubuwan da suka nuna, ya fito fili cewa babu Allah a zuciyarsu. Basu da nufin kirki ga kasarmu. Ni Musulmi ne, kuma ina aiki da koyarwar addinin Kirista ma, ta yin amfani da koyarwar addinan guda biyo domin zaman lafiya da kowa da kowa a duniya.

Ina mai sha’awar jaddada matsayi na, na sukar wannan ta’asa wanda bashi da waje duniyar bil-adama. Addinin Musulunci bai amince da shi ba, kuma babu wannan a cikin Bible.

Ya kamata mutanen nan su sani cewa duniyar wayayyu na adawa da ta’addanci. Muna matukar godiya da duniya take goyawa Najeriya a wannan matsanancin lokaci. Muna fata da addu’a na cewa wadannan yara mata zasu koma wajen iyayensu a kwanaki masu zuwa.

Yayin da gwamnatin Tarayya da sojoji suke aiki domin tabbatar da tsaron ‘yan kasa a wannan lokaci, munyi imanin cewa za’a iya kara matsa lamba wajen gani an tabbatar da tsaron Najeriya da ‘yan Najeriya. Saboda haka muna farin ciki da gwamnatin Tarayya ta amshi taimakon kasa da kasa wajen nemo wadannan dalibai, da kuma kawo karshen ta’addanci a wasu bangarorin Najeriya.

Nayi yaki domin hadin kan Najeriya. A shekaru na masu yawa, ina son tattaba kunne na, da naku tattaba kunnen, da matasa da ma duka ‘yan Najeriya su albarkata daga kasa mai cigaba da hadin kai, da kuma kyamar tarzomar bangaranci a cikin gida, da ma daga kasashen ketare.

Yanzu ba lokacin siyasa bane. Yanzu kuma ba lokacin nuna yatsa bane saboda ban-bancin akida. Hadin kan Najeriya ba abune na wasa ba, kuma babu abunda zai raba mu a matsayinmu na mutanen kasa daya. Saboda haka ina kira ga ‘yan Najeriya a gida, da ma kasashen ketare su goyi bayan kasa a yunkurin da takeyi na kawo karshen hare-hare akan fararen hular da basu ji ba, basu gani ba.

Sai mun ajje a gefe, duk wani buri namu, mun tabbata kasarmu ta hada kanta, ta kwato diyaucinta. Banda ma haka, sanin dukkaninmu ne cewa bamu da wata kasa banda Najeriya da zamu iya kira namu.

Allah Ya albarkaci Najeriya."
XS
SM
MD
LG