“Ofishin jakandancin mu a Abuja a shirye yake ya hada kan kwararru wadanda zasu bada gudunmuwar kwarewa akan harkokin tattaro bayanai, da bincike, da karbar mutanen da akayi garkuwa dasu, da kuma taimakawa wajen rarraba bayanai da taimakawa wadanda tarzoma ta shafa.”
Kakakin Ma’aikatar Harkokin Wajen Amurka Jen Psaki tace taga cikin agajin da Amurka zata baiwa Najeriya harda jami’an sojoji da jami’an ‘yan sanda.
Wani mai baiwa Mr. Jonathan shawara yace shugaban ya gayawa Kerry cewa jami’an tsaron Najeriya na aiki “ba dare ba rana” domin ceto wadannan dalibai, wadanda aka sace su a tsakiyar watan Afrilu, daga makarantarsu ta sakandare dake Cibok, wani dan karamin gari a Jihar Borno dake arewacin Najeriya.
Mai baiwa shugaban kasa shawara Reuben Abati, a wata sanarwa da ya bayar Talatannan yace Shugaba Jonathan ya gana da manyan hafsoshin tsaron kasa bayan ganawa da Kerry.
Misalin sama da dalibai 300 ne aka sace daga makarantarsu a watan da ya wuce. Wasu daga cikinsu sun kubuce, amma har yanzu ba’a ga misalin 276 ba.
A safiyar Talatannan ne, mazauna wani gari dake arewacin Najeriya suka ce suna zaton ‘yan bindigan Boko Haram sun sace musu mata 8 a wannan yanki.
Mazauna garin Waraba Talatannan sunce ‘yan bindiga sun kaiwa kauyensu farmaki Lahadinnan suka sace yara mata. A cewarsu maharan, wadanda suka je a cikin motoci da dama, sun sace abinci da dabbobi a harin