Kasashen dake halartar taron sun hada da Najeriya, Ghana, GuineBissau, Saliyo, Gambia, da Chadi da kuma Liberia da kasar Guinea Conakry.
Ana kuma sa rai cewa wasu kasashen zasu biyo baya kamar Kamaru, Zambia,da Mozambique da sauransu.
Shi dai wanna taron makasudisa, shine domin samar da hanyoyin da za'a bi domin inganta abubuwan more rayuwa a kasashen Afirka ne.
Da harsashen cewa inganta abubuwan more rayuwa zai taimaka akan harkokin tsaro da hana mutane kauracewa kasashensu.