Muhammed Bashir wanda aka fi sani da sunan Muhammed Bashir Tubari mai taimakon gwamnan jihar Borno ta hanyar fadakarwa da hanyar sadarwar zamani ya bayyana takaicin gwamnatin jihar bisa ga abun da yace an yiwa jami'ansu a fadar shugaban kasa.
Muhammed Bashir ya bayyana abun da sanarwarsu ta kunsa. Yace a sanarwar sun nuna rashin jin dadinsu ne akan yadda ofishin shugaban kasa da na uwargidansa suka tada maganar sace daliban Cibok suka kuma wulakantar da su.
Wato fadar shugaban kasa ta gayyaci manyan shugabannin gwamnatin jihar da kuma wasu jami'an tsaro daga jihar ta Borno. A fadar shugaban kasa an ci zarafinsu an kuma kunyatasu a gaban jama'a. Bugu da kari ita gwamnatin tarayya bata nuna damuwa da irin halin da iyayen yaran suka shiga da ma al'ummar jihar gaba daya.
Bisa ga umurnin shugaban kasa an kwashe duk jami'an an kaisu ofishin sifeton 'yan sanda inda aka rikesu na sa'o'i da dama aka kuma sasu suka rubuta jawabai irin wadanda 'yan sanda ke tilastawa masu laifi su rubuta. Bayan sun gama rubutun an sasu su yiwa kansu beli kana aka sake mayarda su fadar shugaban kasa.
Mutanen da aka gayyata daga Bornon sun hada da gwamnan jihar da kwamishanan ilimi da kwamishanan 'yan sandan jihar da daraktan 'yan sandan ciki da shugabar makarantar yaran da aka sace da DPO na garin Cibok da babban maigadin makarantar da shugaban karamar hukumar Cibok. Banda gwamnan duk sauran shugaban kasa ya mikasu ga babban sifeton 'yan sanda.
Bayan duk wannan da aka yi masu, sai kuma washegari aka sake kiransu aka ce matar shugaban kasa na bukatarsu. A can sai da aka sa suka yi tsayuwar sa'o'i hudu akan kafafunsu kafin ta gansu. Da suka zauna da matar shugaban kasa sai tana nuna masu wai karya su keyi ba'a sace yaran ba. Inji matar Jonathan an shirya ne domin a kunyata gwamnatin mijinta.
Ga rahoton Haruna Dauda Biu.