WASHINGTON, DC —
Tsaro da ya kamata a samu a kasashen Afirka wuin yin cinikayya ba tare da tsangwama ba shi ne mahimmancin abun da shugaban Ghana da na Afirka Ta Kudu suka fi maida hankali a kai.
Bayan ganawarsu shugabannin sun yi jawabi ma manema labari a fadar shugaban kasar Ghana. A jawabin marhaban da ya yi shugaban Ghana John Mahaman ya nuna takaicinsa dangane da rashin kasuwanci tsakanin kasashen Afirka. Ya nemi a canza wannan lamarin domin, in ji shi kasuwanci tsakanin kasashen Afirka shi ne maafita ga nahiyar. Abun takaici ne a ce kasuwanci tsakanin kasashen nahiyar na kasa kasa idan aka kwatanta da irin kasuwancin da nahiyar ke yi da kasashen turai da asiya.Ya ce ya zama wajibi kasashen su hada kansu. Shugaban Ghanan ya nuna farin cikinsa da aniyar Afirka Ta Kudu na yin aiki da kasar Ghana a fannin makamshin lantarki.Ya ce jarjejeniyar da suka sama hannu ta hada makamashi.