Jiya lahadi 18 ga watan Disamban 2022 aka yi hidimomin tunawa da ranar da Nijer ta zama Jamhuriya bayan zaben raba gardamar 1958 da ya fayyace a fili cewa jama’a na bukatar ganin kasar ta sami ‘yancin kai daga turawan mulkin mallaka.
Masu rajin kare dimokradiya a jamhuriyar Nijer sun yi na’am da taron da ake shirin farawa a yau Talata 13 ga watan disamba a nan birnin Washington DC a tsakanin kasar Amurka da kasashen nahiyar Afirka.
Yayin da talakawa ke ci gaba da fama da matsalar ruwan sha a Janhuriyar Nijar, masu ruwa da tsaki sun tashi haikan wajen kokarin hada karfi da karfe don magance matsalar.
Wannan na zuwa ne bayan la’akkari da barazanar lalacewar tarbiyar da ake fuskanta a wannan lokaci da kafafen sada zumunta ke zama wani bangare na rayuwar al’ummar kasar.
An tarawa gwamnatin Jamhuriyar Nijar sama da biliyan 45 na euro don gudanar da ayyuakan jama’a har zuwa shekarar 2026.
A cigaba da samun nasara, da wani sa'in akan yi a yaki da ta'addanci, wasu gwamman masu aikata manyan laifuka da makami sun tuba a Janhuriyar Nijar.
A jamhuriyar Nijer wani harin ta’addanci da aka kai a tashar bincike ta ‘yan sandan garin Say dake a km 60 da birnin Yamai ya haddasa asarar rayukan da suka hada da jami’an tsaro da farar hula.
Wasu mutanen da ba a san ko su waye ba sun yi rubuce rubucen da jan fenti akan allunan shaidar titin shugaba Muhammadu Buhari dake birnin Yamai na jamhuriyar Nijar.
A Duniyar wakar Hausa da Janhuriyar Nijar an yi wani babban rashi bayan da shahararriyar mawakiyar nan mai suna Hafsou Garba ta rasu yau.
Hukumomin Nijar sun gudanar da wani taron hadin gwiwa da jakadun MDD da na kungiyar EU da nufin jan ra’ayin masu hannu da shuni akan bukatar samun gudunmowarsu a yunkurin tsarin ciyar da yara a makarantun boko.
Majalisar dokokin Nijar ta yi na’am da kasafin kudaden shekarar 2023 da nufin bai wa gwamnatin kasar cikakkiyar damar gudanar da ayyukan da ta kira na inganta rayuwar al’umma, sai dai ‘yan adawa a majalisar sun juya wa kasafin baya saboda a cewarsu ba a yi la’akkari da halin da kasar ke ciki ba.
Jamhuriyar Nijar, Laraba 30 ga watan Nuwamba ake shagulgulan tunawa da ranar aikin ‘yan jarida ta kasa wacce ta samo asali a shekarar 2012 lokacin da shugaban kasa Mahamadou Issohou a zamaninsa ya saka hannu akan dokar hana kulle ‘dan jarida agidan yari saboda aikinsa.
Yayin da karancin alkama da yakin Ukraine ya haddasa ke ci gaba da janyo tsadar burodi da dangoginsa a sassan duniya, talakawa a Janhuriyar Nijar na ganin wani sa'in ana fakewa da yakin Ukraine ne a kuntata masu.
Shugabanin jam’iyyar PNDS Tarayya na kasashen yankin Kudanci da na tsakiyar Afurka sun gudanar da taro a birnin Yamai a jiya Asabar, wato wata daya kenan kafin a gudanar da babban taron jam’iyyar na kasa wanda zai bada damar zaben sabon shugaban jam’iyyar na kasa da mataimakansa.
Shugabanin kasashe da na gwamnatocin Afrika sun gudanar da taron wuni 1 a birnin Yamai na Jamhuriyar Nijer.
Majalisar dokokin jamhuriyar Nijar ta karyata wasu bayanai da ke cewa ‘yan majalisar sun fara yunkurin kara wa kansu kudaden alawus-alawus duk da yanayin talauci da tsadar rayuwar da al’umma ke fuskanta, kuma a lokacin da matsalar tsaro ta addabi dubban ‘yan kasar a sassa da dama.
Domin Kari