NIAMEY, NIGER - Tada magoya bayan PNDS daga barci don ganin jam’iyyar ta yi galaba a yayin zaben mutanen da za su wakilci ‘yan kasar mazauna kasashen waje a majalissar dokoki shi ne babban makasudun wannan haduwa.
Gomman jagororin magoya bayan jam’iyyar ta PNDS mai mulki daga kasashe bakwai na yankin kudanci da na tsakiyar Afurka ne suka hallara a wannan haduwa dake matsayin ta sake jan damara a yunkurin da uwar jam’iyyar ta sa gaba don ganin sun kara kafa jam’iyyar a sassan duniya.
Zaben cike gurbin kujeru biyar na wakilai ‘yan Nijar da ke kasashen ketare (Diaspora) a majalissar dokokin kasa da ake shirin gudanarwa nan da watanni masu zuwa wani abu ne da magoya bayan PNDS na yankin Kudu da na tsakiyar Afurka ke dauka da matukar mahimmanci.
To sai dai shugaban reshen jam’iyyar a kasar Angola Abdourahamane Sidi Mohamed ya nuna damuwa akan rashin yi wa mazaunan yankinsa rajista a yayin ayyukan rajistar zaben da aka gudanar a watan jiya, saboda haka ya yi kira ga hukumar CENI da ta dubi wannan matsala da idon rahama.
A wani abinda ke matsayin matakin jan damara, taron ya sabunta kwamitin jagorancin rassan wadannan kasashe bakwai, uwar jam’iyyar ta gargadi wadannan shugabanni da su maida hankali wajen ayyukan ci gaban manufofin PNDS.
A karshen watan Disamban dake tafe ne jam’iyar ta PNDS mai mulki za ta gudanar da taronta na kasa a birnin na Yamai don zaben sabon shugaba da mataimakansa.
Saurari cikakken rahoto daga Souley Moumouni Barma: