NIAMEY, NIGER - Tsohon shugaban a lokacin har ma ya sha alwashin ganar da takwarorinsa su bi sahu, sai dai shekaru tara bayan wannan yunkuri kungiyoyin ‘yan jarida na cewa ‘yancin aikin jarida a kasar na cikin mawuyacin hali.
Ganin yadda Jamhuriyar Nijar ke fuskantar koma baya a rahoton shekara-shekara na kungiyar kare hakkin ‘yan jarida ta kasa da kasa wato Reporters Without Boders ne ya sa shugaba Mahamadou Issouhou a zamaninsa ya yi na’am da shawarwarin dake kunshe cikin wani daftarin da aka kira Montagne de la Table a karshen wani taron ‘yan jarida da ya gudana a kasar Afrika ta Kudu.
Mafari kenan hukumomin kula da harkar yada labarai a kasar ta Nijar da kungiyoyin ‘yan jarida ke hidimomin tunawa da wannan rana ta haramta kulle ‘dan jarida a kurkuku akan aikinsa. Babban Editan Jaridar La Roue de l’histoire Ibarhim Moussa ya bayyana mana halin da wannan fanni ke ciki a halin yanzu.
‘Yancin aikin ‘yan jarida dake matsayin ma’unin mizanin Dimikrodiyya kowace kasa wani abu ne da a nan Nijar ake yiwa kallon tamkar irin abinda ‘yan magana ke cewa rijiya ta bada ruwa guga ya hana inji, a cewar sakataren yada labaran gamayyar kungiyoyin ‘yan jarida ta Maison de la Presse Souleymane Oumarou Brah.
Sabanin da ake fuskanta a tsakanin ‘yan jarida da wasu jami’ai a yayin tattaro bayanai wata matsala ce da ke yi wa aikin jarida tarnaki lamarin da ke shafar bukatun al’umma saboda haka aka gargadi kungiyoyi masu zaman kansu akan maganar ayyukan fadakarwa.
A bana, ma’aikatar ministan watsa labarai da gamayyar kungiyoyin ‘yan jarida ta Maison de la Presse sun shirya wa matasan ‘yan jarida gasa da a wani gefe wata mahawwarar da ta maida hankali ne a game da nauyin da ya rataya a wuyan ‘yan jarida wajen ankararda hukumomi bukatun da jama’ar kasa ke fatan ganin an biya masu.
Saurari cikakken rahoto daga Souley Moumouni Barma: