Tun a tsakiyar watan Nuwamban 2022 ne dambarwa akan yunkurin kara wa ‘yan majalisar dokokin kasar Nijar kudaden alawus-alawus ta kunno kai. Yayin da wasu ke ganin dacewar matakin a bisa dalilai na inganta yanayin rayuwar wakilan al’umma wasu kuwa na nuna rashin amincewarsu da abinda suke kira hanyar kara wa kasa larura a wani lokaci da ake cikin mawuyacin hali, wannan ne dalilin da ya sa majalisar ta yi zama a ranar Laraba domin fayyace sassan da ta yi wa gyaran fuska a dokar biyan kudaden alawus din ‘yan majalisa, kamar yadda Honorable Kalla Moutari, shugaban kwamitin ‘yan majalisa mai kula da sha’anin doka ya bayyana.
Ta hanyar wannan zama majalisar na kokarin wanke kanta daga zargin da take fuskanta, dalilin da ya sa ra’ayoyi suka zo daya a tsakanin ‘yan majalisar masu rinjaye da na adawa game da wannan magana ta gyaran fuskar dokar kudaden alawus.
Aikin dan majalisa wani abu ne da ya ta’allaka kan maganar kare hakkokin jama’ar kasa, sanin muhimmancin wannan matsayin ne ya sa ‘yan majalisar dokokin Nijar ke da mafi karancin albashi idan aka kwatanta da takwarorin aikinsu na kasashen yammacin Afrika, inji Honorable Boukari Sani Zilly.
Sabon tsarin biyan kudaden alawus-alawus din da aka yi mahawara a kansa ranar Laraba 23 ga watan Nuwamba ya sami amincewar dukkan ‘yan majalisa 151 da suka halarci zauren majalisar kafin a nan gaba a gabatar wa bangaren zartarwa kudirin don tabbatar da shi a matsayin doka ko kuma a maido da shi don sake yi masa karatu na biyu.
Saurari rahoton cikin sauti: