A jamhuriyar Nijer Farashin biredi ya cira sama da kashi 25 daga cikin 100 na farashin da ake sayar da shi a da. Masu gidajen buga biredi na alakanta wannan mataki da tsadar fulawa a kasuwannin duniya. Sai dai kungiyar ‘yan shayi da biredi tace babu kamshin gaskiya a wannn hujja saboda haka ta yi kiran hukumomi su dauki mataki.
Har I zuwa yammacin lahdi 27 ga watan nan na November ana sayar da sandar biredi akan 200f cfa a wajen ‘yan shayi da biredi sai dai an wayi garin jiya litinin wannan farashi ya tashi zuwa 250f cfa abinda ke nufin an yi karin 50f cfa lamarin da kungiyar masu gidajen buga biredi ke dangantawa da tashin farashin ababen masarufi da ake fuskanta a baya bayan nan a kasuwannin duniya. Malan Mahamadou Hassan shine sakataren kungiyar masu gidajen buga biredi ta kasa baki daya.
Sai dai kungiyar ‘yan shayi da biredi ta yi tur da wannan mataki saboda a cewar shugabaninta ba abinda ya sauya a sha’anin hada hadar fulawa da sauran abubuwan da ake amfani da su wajen sarrafa biredi dan haka ta yi kiran mahukunta su dauki mataki. Alhaji Daouda Tankama shine matemaki na 2 na shugaban kungiyar SYVEDICA ta ‘yan shayi.
Tuni wannan al’amari ya fara haifar da damuwa a wajen magidanta irinsu Ibrahim Kantama da ke ganin an bar su da wasu ‘yan kasuwa suna tsawwala farashin kayan abinci ya son ransu.
Ya zuwa yanzu gwamnatin Nijer ba ta bayyana matasyinta ba akan wannan sabon cece kuce da a halin yanzu ya dauki hankalin kungiyoyiin kare hakkin masaya. Malan Maman Nouri shine Shugaban kungiyar ADDC WADATA.
A ranekun farkon yakin da Russia ta kaddamar a Ukraine ma an fuskanci Karin kudin biredi a Nijer sakamakon abinda aka kira tsadar farashin alkama kafin daga bisani an sake komawa kan farashin farko bayan wata tantaunawar da ta hada ofishin ministan kasuwanci da kungiyar masu gidajen buga biredi da kungiyoyin kare hakkin masaya.
Saurari cikakken rahoton Sule Barma: