Shekaru 64 bayan wannan yunkuri ‘yan kasar ta Nijer na bayyana ra’ayoyi mabambanta game da halin da ake ciki a yau.
Yayinda wasu ke ganin an sami ci gaba wasu kuma na cewa har yanzu da sauran aiki.
Ranar 18 ga watan disamba na daga cikin ranakun da ‘yan Nijer ke dauka da mahimmanci ,kasancewarta mai nasaba da shirin samun ‘yancin kai daga turawan mulkin mallaka sabili haka, idan ta zagayo ake yin waiwaye a dangane da mahimman abubuwan da suka wakana a kasar na ci gaba ko akasin haka.
A nasa ra’ayin mataimakin shugaban gamayyar kungiyoyin fafutika na FSCN Abdou Idi ya ce ci gaban da ake ikirarin an samu a Nijer ba zai bayyana ba a zahiri muddin ba a warware wasu tarin matsalolin da ake buris da su ba.
Jami’in yaki da cin bashin kasashen waje a karkashin inuwar kungiyar RNDD Salissou Amadou ya yaba da ci gaban da Nijer ta samu a fannin tattalin arziki ko da yake yana mai nuna damuwa game da yadda ake kasafta dukiyoyin kasa.
A jawabin da ya yi wa al’ummar kasa albarkacin zagayowar wannan rana, shugaba Mohamed Bazoum, ya yi bitar halin da Nijer ke ciki a yau shekaru 64 da zama jamhuriya.
Matsalolin tsaro da yaki da cin hanci da maganar adalci a shara’a na daga cikin mahimman batuttuwan da ya ayyana shirin jan damara akansu.
Ya kuma gargadi ‘yan kasar akan maganar hadin kai domin sai da shi ake samin ci gaba mai darewa a cewarsa.
Saurari rahoton cikin sauti: