A jamhuriyar Nijar wasu gomman ‘yan bindiga sun ajiye makamai da nufin amsa kiran shugaba Mohamed Bazoum don kawo karshen aika aikar da ake fuskanta a sassan kasar ta Nijer. Ministan cikin gida Hamadou Souley Adamou ya karbi wadannan tsofaffin ‘yan bindiga amadadin gwamnatin kasar.
Kimanin ‘yan bindiga 86 ne cikinsu har da mace 1 suka mika makamansu ga hukumomin kasar Nijer domin bada tabbacin sun tuba daga miyagun ayyukan da suka runguma a can baya kamar su fashi da makami kore garken dabbobi da satar mutane domin neman kudin fansa, safarar makamai da ta miyagun kwayoyi.
A yayin wani bukin musamman da ya gudana da yammacin wannan Litinin 5 ga watan Disamba a kauyen Bangui na gundumar Madaoua ne aka karbi wadannan tsofafin ‘yan takife da makamansu. Suna masu cewa kiran da shugaban kasar Nijer ya yi akan batun zaman lafiya ne ya ganar da su hanyar gaskiya. Mu fara da Kabirou Iliassou, wanda ya yi karin bayani kan tubarsu da afuwar da aka yi masu.
Daga cikin wadanan mutane har da wata mata ‘Yar Dubu da a baya aka kama da laifin bai wa ‘yan bindiga mafaka.
Da yake karbar wadanan mutane, Ministan Cikin Gida Hamadou Souley Adamou ya sake nanata kira ga sauran ‘yan bindigar da ke ci gaba da aika aika su dawo gida, ya na mai bada tabbacin cewa har yanzu kofa a bude take.
Garin Bangui da ke gundumar Madaoua akan iyakar Nijar da Najeriya ta bangaren jihar Sokoto wuri ne da ke zame wa ‘yan ta’addan da suka addabi jihohin arewacin Najeriya tamkar mafaka, saboda haka samun tarin wadanda suka tuba a wannan yanki wani abu ne da ake ganin zai taimaka wajen magance tashe tashen hankulan da ake fama da su a garuruwa da dama .
Saurari cikakken rahoton Sule Barma: