Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Fitacciyar Mawakiyar Nijar Hafsou Garba Ta Rasu


Hafsou Garba
Hafsou Garba

A Duniyar wakar Hausa da Janhuriyar Nijar an yi wani babban rashi bayan da shahararriyar mawakiyar nan mai suna Hafsou Garba ta rasu yau.

A jamhuriyar Nijer fitacciyar mawakiyar nan Hafsou Garba ta rasu a yau Litinin 5 ga watan Disamba a birnin Yamai bayan fama da rashin lafiya makwanni 2 kenan bayan rasuwar mijinta. Zabiya Hafsou Garba ta taka rawa wajen yada al’adun Nijer a ciki da wajen kasar sannan ta yi gwagwarmaya a fannin siyasa abinda ya sa hukumomi suka sha kama ta da nufin nuna bacin ransu a duk lokacin da ta rera wata wakar da ke kunshe da kalamun caccakar manufofin gwamnati.

A daya daga cikin wakokin Hajiya Hafsou, ta yi gargadi ga ‘yan Nijer akan mahimmancin kishin kasa, wannan waka ta rera ta ne a 2014 lokacin da kasar ke cikin yanayin tankiyar siyasa . marigayiya Hafsou Garba ta fara waka a tsakiyar shekarun 1970 lokacin da gwamnatin mulkin soja ta bullo da wani tsarin da ake kira Samaria da zummar zaburar da matasa akan maganar bada gudunmowa a ayyukan ci gaban kasa. Rasuwar wannan ‘yar talika da sunanta ya tsallaka ketare wani babban rashi ne ga daukacin ‘yan Nijer. Adamou Yacouba da aka fi sani da sunan Balck Mailer shine sakataren kungiyar mawakan Nijar, kuma shi ma ya yi juyayi.

Ba’idin maganar waka Hafsou Garba na gabatar da shirye shiryen rediyo don fadakarwa a kan zamantakewar al’umma abinda ya sa ta kafa gidan Rediyon Touraki FM na birnin yamai a shekarar 2006 tashar da ta yi wa lakabin Muryar Mawaka da makada la Voix des Artistes.

Mawaki Maman Sani Maty Adumulmula na tunawa da halayen marigayiyar, (kamar yadda za a ji idan an latsa wurin sauti).

Tun a ranakun farkon tsundumar Nijar tafarkin dimokradiya wato a 1991 Hafsou Garba ta shiga harkokin siyasa inda hankalinta ya fi karkata ga jam’iyyar MNSD ta shugaban kasa Janar Ali Chaibou har I zuwa lokacin da jam’iyyar ta dauki sunan MNSD NASARA a karkashin shugabancin Tanja Mamadou. Bayan jam’iyyar ta dare biyu Hajiya Hafsou ta goya wa Hama Amadou baya inda suka kafa jam’iyar Moden Lumana a 2009. Wakokin da ta ke rerawa jagoran wannan jam’iyya ta ‘yan hamayya sun yi sanadin kama ta sau tari.

Ba’adariyar garin Dogaraoua a jihar Tahoua Marigayi Hafsou Garba ta yi aikin tafreta a wani banki mai zaman kansa kafin ta koma ma’aikatar magajin garin Yamai da aiki. Ta rasu ta na da shekaru 61 a duniya; ta bar ‘yaya 6 da jikoki. Da misalin karfe 3 na ranar wannan Litinin ne aka yi jana’aizarta a nan Yamai.

Saurari cikakken rahoton Sule Barma:

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:27 0:00

XS
SM
MD
LG