Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shugabanin Kasashen Afrika Sun Gudanar Da Taron Wuni 1 A Jamhuriyar Nijar


Taron kungiyar Afirka
Taron kungiyar Afirka

Shugabanin kasashe da na gwamnatocin Afrika sun gudanar da taron wuni 1 a birnin Yamai na Jamhuriyar Nijer.

An gudanar da taron ne da nufin tantauna hanyoyin bunkasa tattalin arzkin kasashen nahiyar wace rashin tsayayyun kamfanoni da masa’antu shekaru 4 bayan da aka cimma yarjejeniyar kasuwanci maras shinge wato ZLECAF ko kuma AFCTA, da nufin shawo kan matsalar karancin ko kuma rashin tsayayyu masana’antu da kamfanonin da za a iya alfahari da su.

Buhari da Bazoum a taron kungiyar Afirka
Buhari da Bazoum a taron kungiyar Afirka

Don haka ne ya sa mafi yawancin kasashen nahiyar na kungiyar AU ta fara yunkurin lalubo mafitar wannan al’amari da ke dabaibaye tafiyar sha’anin tattalain arziki da ya zame dalilin shugabanin kasashe da na gwamnatocin Afrika suka hadu a nan birnin don samo bakin zare.

A hirar shi da Muryar Amurka, Moussa Faki Mahamat shugaban hukumar gudanarwar kungiyar tarayyar Afrika. Yace dukan jerin siyasar da kungiyar AU ta bullo da su a tsawon gomman shekarun da suka gabata, ba su bada wani sakamako mai gamsarwa ba.

Amincewa da kura-kuren da aka fuskanta abu ne da zai bamu damar dagewa da neman hanyoyin inganta sakamakon da muke neman cimma.

Taron kungiyar Afirka
Taron kungiyar Afirka

Idan a wasu kasashe mambobin kungiyar an samu bayyananen cigaba, a wasun kuwa, fannin masana’ntu ya fuskanci turjiya ko kuma ya durkushe kwata kwata, sannan a daya gefe guda kayayakin da ake fitarwa zuwa waje, ba a yi su da fasali irin na cigaban kimiya ba.

Wannan rauni abu ne da ya kamata mu lura da shi a matsayinmu na kasashe mambobin kungiyar AU .

Makuddan kudade ne ke fita daga kasashen Afrika a kowace shekara don odar kayayaki daga kasashe masu arzikin masana’antu sakamakon rashin tsayayyun kamfanin a gida ko a makwafta, alhali yau shekaru a kalla 3 kenan da cimma yarjejeniyar kasuwanci maras shimge ta ZLECAF.

Shugaba Mohamed Bazoum mai masaukin baki na ganin lokaci ya yi da za a lura. Yana mai cewa "shin kuna da masaniya kasata Nijer dake daya daga cikin kasashen da suka yi fice a fannin kiwon dabbobi a Afrika, daga Faransa da Hollande muke odar madara, yayinda su kuma makwaftanmu daga Argentina da New Zeland suke odar nama?"Wannan abu ne dake cike da ban mamaki wadanda babu hujjar faruwarsu. Matsala ce da banda karancin kudaden shiga da take haddasawa, abu ne da ke haifar da karancin aikin yi domin kai tsaye yake shafar makomar kamfanoni da masana’antu a kasashenmu."

Shugaban rikon kungiyar ta AU Macky Sall na Senegal bai samu halartar wannan taro ba saboda dalilan da ba a bayyana ba, amma ya bukaci Paul Kagame na Rwanda ya shugabancin wannan zama a madadinsa.

Yace "muna bukatar ware kudade masu tsoka a kasafin kudaden kasashenmu daban daban domin habbaka masana’antunmu haka kuma wajibi ne mu dauki matakin karfafa hanyoyin samar da makamashi da hanyoyin zirga-zirga, sannan ya kamata mu dauki matakan karfafa alakar aikin dake tsakanin jami’oinmu da masana’ntu masu zaman kansu don ganin an karkatar da akala wajen inganta fannin kirkire-kirkire wadanda zai bai wa matasa damar shiga a dama da su."

Karfafa hanyoyin suhuri na kasa da na sama da na ruwa wata shawara ce da ministar harkokin wajen Senegal Aissata Sall ta gabatar a wurin wannan taro da aka kammala da sanarwar karshen taro.

Saurari rahoton cikin sauti:

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:28 0:00
Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG