A jamhuriyar Nijer rahoton kungiyar addinin Islama ta kasa wato AIN ya yi nuni da cewa an samu raguwar mutuwar aure a birnin Yamai a shekarar 2022 idan aka kwatanta da adadin aurarakin da suka mutu a shekarar 2021.
Gwmnatin mulkin sojan Mali ta sanar da yin afuwa ga wasu sojojin Côte d’Ivoire 49 da ta kama a lokacin da suka sauka a filin jirgin saman Bamako a watan Yulin 2022.
Kasar Amurka ta bai wa jamhuriyar Nijar tallafin jirgin sama samfarin C 130 domin karfafa gwiwa ga sojojin kasar a yakin da suke kafsawa da ‘yan ta’addan yankin Sahel.
Tuni dai wannan al’amari ya haddasa mutuwar dubban kaji, abin da ya sa mahukunta suka dauki matakai don dakile yaduwar cutar.
Hukumomin Burkina Faso sun bukaci Faransa ta canza jakadanta Luc Hallade don maye gurbinsa da wani sabo.
Hukumomi a jamhuriyar Nijer sun cafke wasu manyan jami’an bankin Manoma na BAGRI, saboda zargin rubda ciki akan dubban miliyoyin CFA matakin da ya dauki hankalin kungiyoyin manoma da na jami’an yaki da cin hanci.
Masu sha’awar kwallon kafa a Jamhauriyar Nijar kamar sauran takwarorinsu na sassan duniya sun bayyana alhini a game da rasuwar fitaccen dan kwallon Brazil Pele.
A wani mataki na ganin jama'a sun dada samun kulawa daga gwamnati a Janhuriyar Nijar, an dau wani mataki na ganin cewa shugabannin hukumomin da su ka fi kusa da jama'a sun samu gogewa kan yadda za su yi aikinsu.
Hukumar kare hakkin dan adam a jamhuriyar Nijar ta yi bitar abubuwan da ta ce ta gano a yayin binciken da ta gudanar a mahakar zinaren Tamou dake jihar Tilabery inda wasu jiragen sojan kasar suka yi ruwan wuta a lokacin da suka bi sawun wasu ‘yan ta’adda a ranar 24 ga watan Oktoban da ya gabata.
A jamhuriyar Nijar ‘yan kasar sun bayyana juyayi a game da wani hatsarin da jirgi mai saukar angulu ya yi wanda ya yi sanadin mutuwar sojojin kasar biyu da wani sojan kasar waje lokacin da ya fadi ya kuma kama da wuta a filin jirgin sojan sama dake birnin Yamai a jiya litinin.
Lamarin ya faru ne da misalin karfe 10 da minti 40 na safiyar Litinin 26 ga watan Disambar 2022.
Hukumar kula da fiton kayakin ‘yan kasuwar Nijar daga tashoshin jiragen ruwa zuwa sassan kasar CNUT ta kaddamar da ayyukan fadakarwa domin ganar da manyan ‘yan kasuwar dake oda daga kasashen waje.
Hukumar kula da fitar da kayayakin ‘yan kasuwar Nijer a tashoshin jiragen ruwa, CNUT, ta kaddamar da aiyukan fadakarwa don kaucewa matsalolin kan hanya a wannan lokaci da yakin Russia a Ukraine ke haddasa tsaiko ga harkar sufuri.
Hukumar kare hakkin dan adam ta CNDH ta gabatar wa Majalissar dokokin kasa rahotonta na shekarar 2021 wanda ke fayyace abubuwan da suka wakana masu nasaba da tauye hakkin bil adama a kasar ta Nijer a tsawon shekarar da ta shige.
Yayin da makamashi ke dada tsada a Janhuriyar Nijar, 'yan raji sun yi kira ga mahukunta da su rage ma talaka farashin makamashi.
Hukumar yaki da fataucin miyagun kwayoyi ta Jamhuriyar Nijar, OCRTIS, ta kama wasu yan Najeriya da su ka hadiye miyagun kwayoyi da nufin safararsu zuwa kasar Aljeriya.
Jiya lahadi 18 ga watan Disamban 2022 aka yi hidimomin tunawa da ranar da Nijer ta zama Jamhuriya bayan zaben raba gardamar 1958 da ya fayyace a fili cewa jama’a na bukatar ganin kasar ta sami ‘yancin kai daga turawan mulkin mallaka.
Domin Kari