Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Tankiyar Diflomasiya Na Shirin Barkewa A Tsakanin Burkina Faso Da Faransa


Luc Hallade
Luc Hallade

Hukumomin Burkina Faso sun bukaci  Faransa ta canza jakadanta Luc Hallade don maye gurbinsa da wani sabo.

Wannan na zuwa kasa da mako 2 kenan bayan da suka umurci jakadiyar MDD Barbara Manzi ta fice daga birnin Ouagadougou saboda zarginta da bayar da hasashen karya a game da abin da ka iya zama makomar sha’anin tsaro a kasar ta Burkina Faso mai fama da aika aikar ‘yan ta’adda.

Sai dai masu sharhi na alakanta abin a matsayin wani makircin da Russia take kitsawa don samun gindin zama a yankin Sahel.

Ta hanyar wasikar da suka aikewa ofishin ministan harakokin wajen Faransa a farkon makon nan ne hukumomin Burkina Faso suka bukaci kasar ta canza jakadanta a birnin Ouagadougou Luc Hallade.

Koda yake wasikar ba ta yi bayani akan dalilan nuna wannan bukata ba, wasu majiyoyin gwamnati sun ayyana cewa ana zargin jakada Luc da bai wa Faransawa shawarar gaggauta ficewa daga garin Koudougou dake yammacin Ouagadougou sakamakon lalacewar al’amuran tsaro.

Shugaban kungiyar Mojen Siraji Issa na ganin rashin dacewar wannan mataki.

Wannan na faruwa kwanaki 10 kacal bayan da gwamnatin Capitaine Ibrahim Tarore ta umurci jakadiyar MDD Barbara Manzi ta kwsahe ya-nata- ya-nata daga Burkina Faso bayan da ta yi kiran jami’an MDD su hamzarta kwashe iyalansu daga Ouagadougou.

Haka kuma ana zarginta da yin mu’amula da wasu daga cikin kwamandojin ‘yan ta’adda abin da suka ce shi ke bata damar shiga Djibo hankali kwance duk da kasancewar wannan gari matattarar ‘yan ta’adda.

A cewar Shugaban gamayyar Reseau Esperance, Mahaman Bachar alama ce dake nunin Afrika ta fara farga da tafiyar da ta dace da yanayin da ake ciki a yau a duniya.

Rashin samun wani bayyananen sakamako a yakin da aka shafe shekaru ana kafsawa da ‘yan ta’adda a yankin Sahel wata dama ce da abokan hamayyar kasashen yammaci ke amfani da ita don samun matsugunni a nahiyar Afrika in ji mai sharhi akan al’amuran yau da kullum Abdourahaman Alkassoum.

Saurari rahoton a sauti:

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:06 0:00

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG