NIAMEY, NIGER - Wannan wani yunkuri ne da ke kara jaddada huldar ayyukan soja da ke tsakanin kasashen biyu masu manufa daya akan batun yaki da ta’addanci.
A yayin wani bukin da ya gudana a filin jirgin saman soja Escadrille da ke birnin Yamai ne mukaddashin Jakadan Amurka Susane N’garnim ta damka wa hukumomin tsaron Nijar wannan jirgi samfarin Cargo C 130 domin amfanin sojojin kasar wadanda aka yi amannar cewa suna taka rawa sosai a yakin da ake gwabzawa da kungiyoyin ta’addancin yankin Sahel.
Jami’ar hulda da ‘yan jarida a ofishin jakadancin Amurka a Nijar Aichatou Ambarka ta yi mana magana akan wannan tallafi.
Ministan tsaro Alkassoum Indatou ya yi godiya a madadin gwamnatin Nijar da ma al’ummar kasar baki daya, domin a cewarsa wannan gudunmawa ta gwamnatin Amurka babban alheri ne da ke kara wa kasar ta Nijar karfin soja.
Ya ce samun wannan tallafi na jirgin C 130 abu ne da ke saka rundunar mayakan Nijar a sahun wadanda suka fi takwarorinsu wadatattu kuma ingantattun kayan aikin jigilar soja a kasashen da ke yankin kudancin Sahara. Muna godiya ga Amurka da wannan gudunmowa.
Amurka na kan gaba a jerin kasashen da suke yi wa Jamhuriyar Nijar rakiya a fannonin da suka shafi sha’anin tsaro banda maganar kayan ayyukan soja da Nijar din ke samu irinsu motocin yaki da na’urorin zamani.
Saurari cikakken rahoto daga Souley Moumouni Barma: