Da alamar batun na da nasaba da matakan sulhun da kungiyar ta sa gaba kamar yadda a daya bangare bayanai ke nunin ayyukan fadakarwar da shugabanin addinai da na kungiyoyin masu zaman kansu sun taka rawa wajen samar da wannan sauyi.
A shekarar 2021 aure kimanin 3088 ne kungiyar addinin Islam ta Association Islamique du Niger (AIN ) ta ce sun rabu a birnin Yamai kawai bayan da yunkurin sulhu ya ci tura a tsakanin wadanan ma’aurata to amma kakakin AIN Ustaz Moha Halil Dan Yaro ya shaida mana cewa kididigar dubban karar da aka shigar a ofishin kungiyar a shekarar 2022 ta nuna cewa a wannan karon matsalar ta ja baya da sama da kashi 50 daga cikin 100.
Dimbin dalilai ne aka gano cewa suna haifar da rashin jittuwa a tsakanin ma’aurata har aka kai matsayin da rabuwar aure ta zama tamkar annoba a yau.
Shugabar kungiyar kare hakkin mata da yara kanana SOS FEVF, Madame Ahmed Mariama Moussa na danganta raguwar mutuwar aure a 2022 da wasu tarin matakan da aka dauka bayan tsanantar wannan matsala a shekarar 2021.
Kungiyar AIN ta ce tun a shekarun farkon samun ‘yancin kai gwmanatin Nijer ta dora wa alhakin sulhunta ma’aurata a addinance da rabon gado hakkokin mata da na yara da dai dukkan wasu matsaloli na rayuwa dake tasowa a tsakanin al’umma kan karbar koke koken wadanda ke tunanin an tauye masu hakki irin na zamantakewa koda yake a daya bangare kotuna kan kula da irin wadanan matsaloli a zamanance.
Saurari rahoton a sauti: