Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Nijar: Lugudan Wuta Na Sojoji A Tamou Ya Ritsa Da Fararen Hula Bisa Kuskure - Rahoto


Nijar: Kwamitin Binciken Farmakin Mahakar Tamou Ya Fitar Da Rahotonsa
Nijar: Kwamitin Binciken Farmakin Mahakar Tamou Ya Fitar Da Rahotonsa

Hukumar kare hakkin dan adam a jamhuriyar Nijar ta yi bitar abubuwan da ta ce ta gano a yayin binciken da ta gudanar a mahakar zinaren Tamou dake jihar Tilabery inda wasu jiragen sojan kasar suka yi ruwan wuta a lokacin da suka bi sawun wasu ‘yan ta’adda a ranar 24 ga watan Oktoban da ya gabata.

NIAMEY, NIGER - To sai dai wasu masu fafutika na cewa ba su gamsu da bayanan hukumar ba.

Nijar: Kwamitin Binciken Farmakin Mahakar Tamou Ya Fitar Da Rahotonsa
Nijar: Kwamitin Binciken Farmakin Mahakar Tamou Ya Fitar Da Rahotonsa

Tun a washe garin farmakin da sojin suka kai a mahakar Tamou, hukumar kare hakkin dan adam ta CNDH ta kafa wani kwamitin kwararru domin gudanar da binciken da zai bada damar zakulo gaskiyar lamarin sakamkon dambarwar da ta barke a tsakanin masu cewa daruruwan mutane ne suka halaka sanadiyar luguden wutan, a dayan gefen kuma, wasu suka aminta cewa mutane bakwai suka rasu wasu 25 suka ji rauni kamar yadda hukumomi suka sanar.

Binciken na tsawon kawanki 10 ya tabbatar da sojin sun yi barin wuta a kusa da wannan mahaka sai dai girman barnar da abin ya haddasa bai kai yadda aka yi ta yayatawa ba.

Hukumar ta ce sun sami izinin tattara takardun mutanen da harin na mahakar Tamou ya rutsa da su don a biya su diyya.

Nijar: Kwamitin Binciken Farmakin Mahakar Tamou Ya Fitar Da Rahotonsa
Nijar: Kwamitin Binciken Farmakin Mahakar Tamou Ya Fitar Da Rahotonsa

Da ma tun a ranar farkon bayyanar labarin samamen da jiragen sojan Nijar suka kai a mahakar Tamou, masu fafutika ke matsa lambar ganin an samar da haske.

Haka dai ita ma gamayyar kungiyoyin M62 a ta bakin shugabanta Abdoulaye Saidou ke cewa binciken na CNDH ya yi ragi.

Hare haren da aka kai wa jam’ian tsaro a tashar bincike ta Tamou a ranakun Asabar 22 ga watan Oktoba da Lahadi 23 ga watan, wadanda suka haddasa mutuwar ‘yan sanda 2 da jikkata 1 tare da sace makamai ne ya sa jiragen soja suka yi ruwan wuta a kan wasu runfunan da aka hango ‘yan ta’adda suna kokarin boye makaman da suka sata lamarin da ya firgitar da masu hakar zinare, wasu suka tsere saura suka buya a rijiyoyin zinare.

Saurari cikakken rahoto daga Souley Moumouni Barma:

Nijar: Lugudan Wuta Na Sojoji A Tamou Ya Ritsa Da Fararen Hula Bisa Kuskure - Rahoto.MP3
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:05 0:00

Zaben 2023

TASKAR VOA: Hira Ta Musamman Kan Tasirin Da Zaben Donald Trump Zai Yi A Harkokin Kasashen Duniya.
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:50 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Ra'ayoyin Wasu 'Yan Nijar Kan Nasarar Donald Trump A Zaben Amurka
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:47 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG