Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Nijar: An Kafa Ma'aikatar Horar Da Shugabannin Kananan Hukumomi Kan Makamar Aiki


Bazoum Mohamed
Bazoum Mohamed

A wani mataki na ganin jama'a sun dada samun kulawa daga gwamnati a Janhuriyar Nijar, an dau wani mataki na ganin cewa shugabannin hukumomin da su ka fi kusa da jama'a sun samu gogewa kan yadda za su yi aikinsu.

Gwamnatin jamhuriyar Nijar ta bada sanarwar kafa wata ma’aikatar horar da shugabannin kananan hukumomi dabarun aiki, musamman abin da ya shafi tafiyar da kudade, sakamakon lura da yadda rashin sanin makamar aiki a wajen Magadan Gari da dama ke haddasa tarnaki wa cigaban kananan hukumomi.

Shekaru a kalla 18 bayan soma shimfida tsarin sakar wa kananan hukumomi ragama, ko kuma ba su kwaryakwaryar ‘yancin cin gashin kai, bayanai na nuna cewa har yanzu ana fuskantar kwan gaba kwan baya wajen tabbatar da wannan tsari wanda ainahi an bullo da shi ne da nufin kusantar da talaka da hukuma, dalili kenan gwamnatin Nijar ta yanke shawarar kafa wani sashen kula da sha'anin horar da Magadan Gari a fannin dabarun aiki ta yadda za a kauce wa kurakuran da aka yi fama da su a baya. Malan Oumarou Moussa shi ne babban darektan hukumar DGDCT, kuma ya yi karin haske.

Magajin Garin Ourafane da ke yankin Maradi, Malan Nafiou Habou, na cewa matakin gwamnatin tamkar faduwa ce ta zo dai dai da zama.

Shi ma Magajin Garin Tahoua bugo da kari shugaban kungiyar magadan gari ta kasa baki daya, Abdou-Raoufou Dodo, ya yaba da wannan mataki koda yake a cewarsa karancin hanyoyin samar da kudaden shiga ga asusun kananan hukumomi ita ma wata matsala ce ta daban da ke bukatar dubawa.

A sheakarar 2004 ne Nijar ta bullo da tsarin sakin ragama ga kananan hukumomi da nufin kusantar da talaka da ma’ikanta sai dai Magadan Gari da dama sun fuskanci fushin hukuma sakamakon rashin sanin makamar aiki ko zargin karkata akalar kudaden da’irorinsu.

Saurari rahoton Souleyman Barma:

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:52 0:00

Zaben 2023

TASKAR VOA: Hira Ta Musamman Kan Tasirin Da Zaben Donald Trump Zai Yi A Harkokin Kasashen Duniya.
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:50 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Ra'ayoyin Wasu 'Yan Nijar Kan Nasarar Donald Trump A Zaben Amurka
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:47 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG