Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Sojojin Jamhuriyar Nijar Biyu Da Wani Na Kasar Waje Sun Mutu A Hadarin Jirgi A Yamai


Wasu sojojin Nijar da takwarorinsu na kasashen waje
Wasu sojojin Nijar da takwarorinsu na kasashen waje

Lamarin ya faru ne da misalin karfe 10 da minti 40 na safiyar Litinin 26 ga watan Disambar 2022.

Ma’aikatar tsaron Jamhuriyar Nijar ta ba da sanarwar mutuwar wasu sojojin kasar 2 da wani dan kasar waje 1 bayan da jirgin mai saukar ungulu mai lamba MI-17 da ke dauke da su ya fadi.

Jirgin ya sam tangarda ne a daidai lokacin da yake kokarin sauka a filin jirgin sojan sama na birnin Yamai.

Lamarin ya faru da misalin karfe 10 da minti 40 na safiyar Litinin 26 ga watan Disambar 2022.

Hukumomin sun ce jirgin ya dawo ne daga wani atisaye da ya halarta.

Sanarwar ta kara da cewa yunkurin ceto wadanan sojoji daga gobarar da ta tashi bayan faduwar wannan jirgi ya citura.

Tuni aka kafa kwamitin bincike domin gano mafarin wannan mummunan hatsari.

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG