La’akari da wahalhalun da ‘yan kasuwar Nijer masu shigar da kaya daga kasashen waje ke fuskanta, ya sa gwamnatin kasar kafa hukumar Conseil Nigerien des Utilisateurs des Transports CNUT don ba su kariya daga matsalolin da ka iya tasowa.
Malan Yazi Abdou dake zaman jami’in hukumar, ya ce ganin yadda har yanzu ‘yan kasuwa da dama ba su da masaniya a game da alakar aikin dake tsakaninsu da CNUT musamman a jihohi ya sa hukumar kaddamar da aiyukan tuntuba da fadakarwa.
Sakataren kungiyar ‘yan kasuwar Import Export Chaibou Tchombiano, wanda ya nuna gamsuwa da shawarwarin ya kuma bada shawarar karawa wannan hukumar karfin, ganin yadda take sa ido tun daga fitowar kaya har zuwa cikin ‘kasa.
Jamhuriyar Nijer dake tsakiyar yankin sahel na fama da tarin kalubale wajen shigo da kayayaki, sakamakon rashin tashar jirgin ruwa lamarin da ke shafar sha’anin kasuwanci saboda wahalwalun kan hanya masu nasaba da harkokin dakon kaya, dalilin da ya sa hukumomin kasar kulla yarjejeniya da kasashe makwafta dake gabar teku, to amma duk da haka har yanzu da sauran rina mafarin kafa wannan hukuma ta CNUT kenan don kare hakkokin ‘yan kasuwar kasar a ketare.
Domin Karin bayani saurari rahotan Sule Muminu Barma.