Hukumar yaki da cutattuka masu yaduwa ta Najeriya wato NCDC ta bayyana cewa kimanin mutane 790 suka kamu da cutar korona birus a kasar.
Mazauna yankin Mpape dake babbar Birinin tarrayyar Najeriya Abuja sun koka game da Rushe shaguna har da gidajen da Gwamnatin babbar birnin take yi.
Jagororin kwamitin rikon Jam’iyyar APC sun fitar da sanarwa a hukumance kan hukuncin kotun koli na tabbatar da halarcin kwamitin riko na jam'iyyar APC
Majalisar Zartarwa ta Najeriya ta amince da ta ba da kwangilar gyaran matatun mai da ke Warri da ke kudu, da Kaduna a Arewacin kasar, a kan kudi Dala biliyan 1.4.
Gwamnatin tarayyar Najeriya ta ce ta dukufa sosai wajen tabbatar da an kammala aikin shata iyakar ta da kasar Kamaru.
Bayanai na baya-bayan nan daga Najeriya na nuni da cewa an sami karin adadin wadanda suka kamu da cutar Corovirus da ya haura 500 a karon farko a rana guda cikin watanni hudu bayan bullar sabuwar nau’in cutar na Delta a kasar.
Majalisar Dattawa ta umarci Ofishin Akanta Janar na Tarayya Najeriya da ya dawo da kudi Naira biliyan 665.8 da aka karkatar daga asusun bunkasa fannin ma’adanai na kasar.
Jami'an hukumar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi a Najeriya (NDLEA) sun yi nasarar kama wasu mata biyu wadanda ake zargi da saffarar miyagun kwayoyi.
Albarkacin murnar bikin babban sallah na bana da al'ummar Musulmi suka gunadar a ranar Talata, Gwamnar Jihar Kano Abdullahi Umar Ganduje ya yi wa fursunoni 136 afuwa daga kurkukun jihar.
Hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta Najeriya, EFCC, ta kaddamar da wata manhaja ta wayar salula, wacce za ta rika amfani da ita a wajen aikin yaki da ayukan cin hanci da rashawa a kasar.
Watanni shida bayan rahoton cibiyar bincike ta kasa-da-kasa, mahukunta a Najeriya da kasar Ghana za su kafa wata doka ta musamman da za ta kawo karshen takaddamar kasuwanci dake tsakanin kasashen biyu da ke zama kawaye a cikin yankin Afirka ta yamma.
Gidauniyar Bill da Melinda ta bayar da tsabar kudi dalar Amurka biliyan 2 da miliyan 100 don tallafawa mata ta haujin habaka tattalin arziki, karfafa lafiyar mata da yara mata da kuma aikin daidaita iyali.
A kokarin maido da martabar Najeriya a idon duniya, bisa la’akari da dimbin matsalolin da kasar ke fuskanta, wata kungiya mai rajin zaman lafiya da cigaban kasa wato ta gudanar da taron masu ruwa da tsaki don lalubo da hanyoyin samar da zaman lafiya mai dorewa.
Gamayyar kungiyoyin Arewacin Najeriya (CNG) ta gurfanar da gwamnatin Najeriya a kotu kan kin karba bukatar 'yan kabilar Ibo da ke fafutukar ballewa daga Najeriya don kafa kasar Biyafara.
Kamfanin man fetur na Najeriya NNPC, ya bayyana cewa zai hada hannu da hukumomin tsaro da sauran masu ruwa da tsaki don dakile matsalar fasa kwaurin albarkatun man fetur da satar danyen mai a kasar.
Kasar Canada ta ce za ta ba da tallafin kudi dalar Amurka miliyar 27, domin agazawa wadanda rikicin Boko Haram ya shafa a Najeriya.
A wani yunkuri na ganin an sami sauyi da kuma neman goyon baya ga abin da suka kira juyin mulkin da bai dace da tsarin shugabancin kasarsu ba, al'umar kasar Chadi dake zaune a Najeriya sun gudanar da wata zanga-zangar lumana a gaban Ofisoshin diplomasiya na wasu kasashe a Abuja.
Taron wanda ya gudana a babban birnin tarrayar Najeriya na Abuja, ya tabo batutuwa da dama da suka bayyana halin kunci da al’ummar Fulani ke fuskanta a fadin kasar a cewar shugaban kungiyar ta kasa Alhaji Muhammadu Kiruwa.
Tsohon gwamnar Jihar Imo Rochas Okorocha ya ce sam basu dauki fafatukar da tsagerun kungiyar IPOB ke yi da wani muhimmaci ba, kuma basu dauka za ta girma har ta zama damuwa ga Najeriya ba.
Domin Kari