Majalisar kula da harkokin addinai ta Najeriya NIREC ta kalubalanci Gwamnatin kasar da ta kara kaimi wajen magance matsalar rashin tsaro da ke addabar kasar wadda wani sa’ilin ake dangantawa ko dora laifin ga wata kabila ko addini.
Tsokacin na zuwa ne a daidai lokacin a ci gaba da kai hare-hare da Isra'ila da Hamas ke yi wa junansu, wadanda suka yi sanadiyyar asarar rayukan fararen hula a bangarorin biyu.
Sauran mutum biyun da ake nema sun hada da Tarry Rufus da kuma Bola Ogunsola kamar yadda jaridun kasar suka ruwaito.
Gwamnatin Tarayyar Najeriya ta sake kakaba dokar takaita zirga-zirga, biyo bayan karuwar asarar rayuka da adadin masu kamuwa da cutar Covid-19 a wasu kasashe a fadin duniya, da kuma hatsarin da hakan ke haifarwa ga nahiyar Afirka.
"Mun zo ne don mu roki gwamnatin su taimaka su kubutar mana da 'ya'yanmu, ai ko dabbarka ce ta bata za ka shiga damuwa, ballantana yaronka da ka haife su."
Gwamnatin tarrayar Najeriya ta bayyana takaicinta bisa kasa cimma kudirinta na yi wa kashi biyu bisa uku na al’ummar Najeriya da suka cancanci a yi musu allurar rigakafin cutar coronavirus nau’in Astrazaneca kashi na farko.
Masana a fannin tsaro a Najeriya sun bayyana cewa akwai jan aiki a gaban Sabon mukaddashin babban Sufeton 'yan sandan kasar Usman Alkali Baba a kuma daidai lokacin da shi kuma ya dauki alwashin bullo da sabbin dabarun yaki da 'yan ta'adda.
Yayin da mabiya addinin Krista a fadin duniya ke kammala shagulgulan bikin Easter wato ranar tunawa da gicciyewa da kuma tashin Yesu Almasihu daga cikin matattu a ranar Litinin.
Kungiyoyi masu zaman kansu a Najeriya sun dukufa wajen taimakawa gwamnati a kasar don ganin an samar da wata cikakkiyar doka ko tsari da za su sa a dawo da dukiyoyi da aka kwato daga kasashen ketare.
Tallafi ga mata ne kaidai hanyar bunkasa kasuwancin kasa.
A daidai lokacin da aka fara yi wa rukunin farko na ma’aikatan kiwon lafiya allurar riga-kafin coronavirus ta AstraZeneca a Najeriya, ana samun mabanbantan ra’ayoyi game da riga-kafin.
Najeriya ta kara kimanin Mutane da aka daura akan maganin yaki da cutar kanjamau musamman a yankin da aka fi daukar cutar.
Hukumar bada lamuni ta Duniya IMF, ta shawarci gwamnatin Najeriya ta kara kudaden harajinta na VAT daga kashi bakwai da rabi cikin dari zuwa kashi goma cikin dari nan da shekara daya.
Kungiyar manoma da masu sarrafa masara da sayar da ita a Najeriya ta bayyana cewa tana da isassun masarar da za ta wadaci al’ummar kasar a wannan shekarar duk kuwa da kalubalen da annobar Coronavirus ta kawo ga harkokin noma a kasar.
A karon farko gwamnatin tarrayar Najeriya ta kaddamar da motoci da ke amfani da wutar lantarki a maimakon man fetur, hakan na zuwa ne Karkashin hukumar da ke sa ido wajen ci gaba da zane-zanen motoci ta kasar wato NADDC.
Domin Kari