Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Gidauniyar Bill Da Melinda Ta Tallafawa Mata Da Dala Biliyan 2.1 A Najeriya Da Ma Duniya Baki Daya


Bill and Melinda Gate
Bill and Melinda Gate

Gidauniyar Bill da Melinda ta bayar da tsabar kudi dalar Amurka biliyan 2 da miliyan 100 don tallafawa mata ta haujin habaka tattalin arziki, karfafa lafiyar mata da yara mata da kuma aikin daidaita iyali.

Shirin zai kuma bullo da hanyoyin bunkasa ayyukan da za su ba mata kwarin gwiwar shiga a dama da su a sha'anin shugabanci a Najeriya da duniya baki daya.

A cewar Gidauniyar za'a raba kudaden ne a cikin shekaru biyar masu zuwa.

Wannan kuma wani bangare ne na matsayar taron na samar da daidaito na zamani da matan majalisar dinkin duniya suka shirya tare da hadin gwiwar shugabannin kasashen Mexico da Faransa.

Ana gudanar da taron zauren matan ne daga ranar 30 ga watan Yuni zuwa 2 ga watan Yuli na shekarar 2021 a kasar Faransa.

Taron da ya hada hancin shugabannin kasashe daban-daban, kamfanoni masu zaman kan su, da abokan hulda na farar hula don yin wasu ayyuka na musamman tare da sanar da ba da tallafin kudi, siyasa da shirye-shiryen da za su hanzarta samun daidaito tsakanin jinsi da kuma inganta ayyukan nemawa mata 'yanci.

Tallafin na dala biliyan 2 da miliyan 100 zai bunkasa ayuka a fannoni uku da suka hada da fannin karfafa tattalin arziki da zai lakume dala miliyan 650, fannin kiwon lafiya da tsara iyali zai ci dala biliyan 1 da miliyan 400, yayin da kuma hanzarta shigar mata a sha'anin jagoranci zai lakume dala miliyan 100 a cikin sama da shekaru biyar, sai kuma dala miliyan 230 a cikin sama da shekaru 10.

An dade ana ta gwagwarmayar neman daidaiton jinsi a kasashen duniya a shekaru da dama, saidai wannan gwamgwarmayar na ci gaba na tafiyar hawainiya.

"Yanzu lokaci ya yi da za’a sake farfado da ayyukan neman daidaiton kawo canjin gaske" in ji Melinda French Gates, mataimakiyar shugaban Gidauniyar Bill da Melinda Gates.

Melinda ta kara da cewa, kyawun aikin da su ke yi na daidaiton jinsi shi ne kowane dan Adam zai ci moriyarsa, haka kuma ta ce ya zama wajibi su yi amfani da wannan lokacin don gina kyakkyawar makoma.

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG