Kungiyar Makiyaya ta Miyetti Allah a Najeriya ta gudanar da wani taron da ya hada shugabaninta daga duka sassan jihohin kasar 36 ciki har da Abuja.
Maksudin taron a cewar shugabannin shi ne, a jawo hankalin gwamnati da masu ruwa da tsaki don neman mafita bisa abin da ta kira a take hakkin 'yancin al’ummar Fulani, cin zarafi da kuma barnata dukiyoyinsu da salwantar da rayukan yara da manya yan’ kabilar Fulani.
Kungiyar ta ce ta fi fuskantar wadannan matsaloli ne a jihohin yankunan kudu maso gabashin kasar da kudu maso yammaci.
Shugaban kungiyar a yankunan kudu maso gabashin Najeriya da a 'yan kwanakin da suka gabata aka yi ta fuskanta matsalar tsaro tsakanin makiyaya da manona da kuma hare- haren yan kungiyar IPOB da ya kai ga asarar rayuka da dukiyoyi.
A karshe kungiyar ta bukaci dukkan kabillar Fulani a fadin kasar da su kasance masu hakuri da bin doka tare da kira ga sauran al’uma masu kishin kasa da su hada hannu wajen magance wannan matsalar da kasar ke fama da ita.
Saurari rahoto daga Shamsiyya Hamza Ibrahim: