Akalla shaguna har da gidaje dubu biyu ne hukumar birnin tarayya Abuja ta rusa a yankin na Mpape da ke kusa da gundumar Maitama a Abuja.
Mafi akasarin gine ginen da a ka rusa na yan’kasuwa ne da ke zama a gefen hanya, wadanda hukumar ta ce suna kawo cikas ga zirga-zirgar ababen hawa.
A cewar wata mazauniya yankin ‘’Maman Aisha’’mutane da dama sun tafka asara tare da shiga cikin halin ni yasu
To sai dai hukumar ta ce ta rusa gine-ginen ne saboda an yi su ba bisa ka’ida ba mussaman wadanda ke kan hanyoyi.
Wannan mataki dai ya biyo ne bayan sanarwar gargadi da gwamnati ta yi wa al’ummar yankin watanni uku da suka gabata kafin gudanar da wannan aiki na rusau din a ranar Laraba.
Shugaban riko na Hukumar da ke sa ido kan tsare-tsare a babban birnin tarayya Abuja Garba Kwamkur, ya shaida wa wakiliyarmu cewa matakin hakan ya biyo bayan yawan korafe-korafe da ake samu kan matsalar tsaro a yankin, da kuma bin tsarin da aka shinfida tun sadda aka kirkiro birnin na Abuja wanda ya ba da dama a fadada hanyoyi a yankin.
Idan za’a iya tunawa cikin wata wasika da Ministan shari’a na wancan lokacin Mohmmed Adoke ya rubuta a watan Agusta na shekarar 2012, ya ba da shawarar kada a rushe gidaje da ke yankin na Mpape har sai an shigar da kara gaban babban kotun tarayya.
Wannan dai ba shi ne karo na farko da Mazauna yankin su ka ta ba fuskantar rusau na shaguna da gidaje ba, inda mafi akasari ke zama wajen neman abincinsu.
Gwamnatin Abuja ta bayyana cewa rashin bin tsari da ka’idoji ke jefa al’umma cikin wannan yanayi ga kuma uwa uba matsalar tsaro da ake fama da shi a yankin.
Shugaban Kungiyar yan kasuwar Panteka Musa Abdullahi ya ja hankalin yan kasuwar da lamarin ya shafa da su dau dangana, to amma kuma ya yi kira ga gwamnati kan a cika musu alkawarin da ka dauka na basu wani waje da za su ci gaba da gudanar da harkokinsu na kasuwanci
Ko da ya ke bayanai sun yi nuni da cewa nan gaba za'a kara rushe wasu gine-ginen don fadada manyan hanyoyi, kuma yankunan da lamarin zai shafa sun hada da lugbe, Dutse Makaranta, da kuma Ushafa
Saurari rahoton Shamsiyya Hamza Ibrahim