Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Gamayyar Kungiyoyin Arewa Na Bukace Da Kafa Kasar Biyafara; Sun Maka Gwamnatin Najeriya Kotu


Yan Biafra na Zanga Zanga a Wajen Fadar White House Da Zuwan Buhari.
Yan Biafra na Zanga Zanga a Wajen Fadar White House Da Zuwan Buhari.

Gamayyar kungiyoyin Arewacin Najeriya (CNG) ta gurfanar da gwamnatin Najeriya a kotu kan kin karba bukatar 'yan kabilar Ibo da ke fafutukar ballewa daga Najeriya don kafa kasar Biyafara.

Gamayyar kungiyoyin na Arewacin Najeriya sun shigar da karar ne a gaban babbar kotun tarayya da ke Abuja, inda suke karar Ministan Shari’a Abubakar Malami da Shugaban Majalisar Dattawa Ahmad Lawan da kuma Kakakin majalisar wakilai Femi Gbajabiamila.

Kungiyoyin na bukatar kotun da ta ba da umarnin gaggauta dakatar da bita da ake yi na sake fasalta kundin tsarin mulkin kasar, a kuma soma nazarin hanyoyin baiwa yan kabilar Ibo da ke fafutukar ballewa daga Najeriya damar kafa kasarsu ta Biyafara.

Da yake zantawa da manema labarai a Abuja, shugaban kwamitin aminttatu na gamayyar kungiyoyin Nastura Ashir Shariff ya jaddada matsayarsu na cewa maimakon a ci gaba da yin nazari kan sake fasalta kundin tsarin mulki kasar, kamata ya yi masu wannan aikin su hanzarta samar da hanya mafi sauki da zai baiwa masu fafutukar kafa kasarsu ta Biyafara damar ballewa daga Najeriya kamar yadda su ka bukata.

Tun dai daga ranar 11 ga watan nan na Yuni gamayyar Kungiyar ta bukaci majalisar kasar da ta dakatar da aikin da take yi na sake duba kundin tsarin mulki kasar don baiwa Gwamnati damar shirya zaben raba gardama kan tabbatar da Jamhuriyar Biyafara daga Najeriya.

Ta kuma bukaci majalisar da ta shirya dokar gaggawa ta gudanar da zaben raba gardama don tabbatar da kafa kasar Biyafara a matsayin matakin karshen na raba yan kabilar Ibo da sauran yan Najeriya.

Kungiyar ta yi ikirarin cewa ire iren tashe-tashen hankula da tsagerun kungiyoyi daga yakin kudu maso gabashin kasar ke yi duk bai rasa nasaba da neman kafa kasarsu ta Biyafara.

Akan haka gamayyar kungiyoyin ke ganin kamata ya yi a saurari bukatar ta su, a kuma duba yiwuwar ba su damar ficewa daga Najeriyar, ta yadda za'a sami zama lafiya.

Haka kuma sun bukaci gwamnatin Najeriya da ta gayyaci Majalisar Dinkin Duniya da kungiyar Tarayyar Afirka ta AU da Kungiyar Tattalin Arzikin Kasashen Afirka ta Yamma (ECOWAS), don fara aiwatar da shirye-shirye da za su ba da dama ga masu neman fita daga Najeriya don kafa kasarsu, ta hanyar yin amfani da yarjejeniyoyi da ƙasashe da dama suka amince dasu wanda kuma Nijeriya na daga kasashen da suka sanya hannu a kai.

Saurari Muryar Nastura Ashir Sheriff:

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:19 0:00


Zaben 2023

TASKAR VOA: Hira Ta Musamman Kan Tasirin Da Zaben Donald Trump Zai Yi A Harkokin Kasashen Duniya.
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:50 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Ra'ayoyin Wasu 'Yan Nijar Kan Nasarar Donald Trump A Zaben Amurka
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:47 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG