Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Gwamnatin Tarayya Za Ta Gyara Matatun Mai Na Warri Da Kaduna Kan Dala Biliyan 1.4


 Photo of the Kaduna State refinery in north-west Nigeria
Photo of the Kaduna State refinery in north-west Nigeria

Majalisar Zartarwa ta Najeriya ta amince da ta ba da kwangilar gyaran matatun mai da ke Warri da ke kudu, da Kaduna a Arewacin kasar, a kan kudi Dala biliyan 1.4.

Ministan albarkatun mai na Najeriya, Timipre Sylva ne ya sanar da haka bayan taron Majalisar a ranar Laraba a Abuja, inda ya ce Majalisar ta amince da a kashe Dala biliyan 1.4 domin gyaran matatar mai da ke Kaduna da kuma Warri wanda aka ba kwankilar aikin ga kamfanonin Saipem SPA da kuma Saipem Contracting Limited.

Kasafin kwangilar ya nuna cewa Gyaran matatar mai ta Kaduna zai lakume Dala miliyan 586.9, yayin da ta Warri kuma za’a kashe mata Dala miliyan 897.7.

Ministan ya ce za’a gudanar da aikin ne cikin kashi uku.

A cewarsa “za'a kammala kashin farko a cikin watanni 21, na biyu kuma a cikin watanni 23, sai kashi na uku da za'a kammala gayan a cikin watanni 33.”

Haka kuma Majalisar Zartarwar ta kasa ta amince da gwamnati ta sayi kashi 20 cikin 100 na hannun jarin Matatar Mai ta Dangote a kan Dala biliyan 2.76.

Game da aikin gyran Matatar Mai ta Fatakwal da a aka bayar tun da farko, Sylva ya ce ’yan kwangilar sun riga sun fara aikin, bayan an biya su kashi 15 cikin 100 na kudaden aikin.

Idan za’a iya tunawa, a watan Maris ne Majalisar Zartaswar ta amince da kashe kusan Dala biliyan 1.5 domin gyaran matatar man ta Fatakwal, wadda ita ce mafi girma a Najeriya.

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG