Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ana Dada Samun Masu Kamuwa Da COVID-19 A Najeriya Musamman A Jihar Legas


Dr. Chikwe Ihekweazu, darektan hukumar NCDC a Najeriya
Dr. Chikwe Ihekweazu, darektan hukumar NCDC a Najeriya

Bayanai na baya-bayan nan daga Najeriya na nuni da cewa an sami karin adadin wadanda suka kamu da cutar Corovirus da ya haura 500 a karon farko a rana guda cikin watanni hudu bayan bullar sabuwar nau’in cutar na Delta a kasar.

A safiyar yau Alhamis ne hukumar yaki da yaduwar cututtuka ta Najeriya - NCDC, ta fitar da adadin da ke nuni da cewa an sami mutane 535 dauke da cutar a jiya Laraba.

Hukumar ta NCDC ta bayyana wannan adadi na mutane 535 da suka kamu da cutar da cewa ya zarce adadin mutane 404 da aka samu na ranar 27 ga watan Yuli, adadin da hukumar ta rawaito cewa shi ne mafi yawa a aka samu rana daya a cikin watanni hudu a kasar.

Kazalika hukumar lafiya a matakin farko ta bayyana cewa Jihar Legas ce ke kan gaba cikin jihohin da ke da yawan wadanda suka kamu da cutar.

Hukumar ta kuma bayyana alhininta akan rasa mutane biyar sakamokon cutar a Jiya Laraba.

Wannan kuma ya sa jumlar adadin wadanda aka rasa ya kai 2,139 a kasar baki daya.

TASKAR VOA: Ra'ayoyin Wasu 'Yan Nijar Kan Nasarar Donald Trump A Zaben Amurka
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:47 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Hira Ta Musamman Kan Nasarar Donald Trump Da Kayen Da Kamala Harris Ta Sha
please wait

No media source currently available

0:00 0:04:56 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Yadda Shugabannin Kasashen Nahiyar Turai Suka Taya Donald Trump Murnar Lashe Zabe
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:55 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA

Zaben 2023

TASKAR VOA: Ra'ayoyin Wasu 'Yan Ghana Kan Nasarar Donald Trump A Zaben Amurka
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:40 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Yadda Trump Da Magoya Bayanshi Suka Yi Murnar Lashe Zabe
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:27 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG