Yan’ kasar ta Chadi sun bayyana damuwarsu wajen neman kasashen da suka ci gaba a duniya da kuma wadanda ke cin moriyar tsarin demokradiya, da su bi sahun al’ummarsu wajen yin Allah wadai da irin tsarin mulkin soji da ke gudana a kasarsu, tare da neman a gaggauta kafa gwamnatin farar hula ta demokaradiya.
Ibrahim Zain Congy dan gwakwarmaya ne kuma jagoran masu zanga- zangar, ya fadawa Muryar Amurka cewa ‘’a kasar Chadi tsohon shugaba na mulki kama karya marigayi Idriss Debby, kasar Faransa ce ta dauki nauyinsa ta ke kuma mara masa baya ake mana mulkin danniya. Tun shekarar 1991 muke shan wuya, mu ke fama da rashin adalci’’.
Kasar ta Chadi dai ta yi kaurin suna a matsalar tawaye da hare-haren yan bindiga, da kuma zargin dadadden mulkin danniya da kama karya, wanda yan kasar ke gannin har yanzu basu fita daga zamanin mulkin mallaka ba a karkashin kasar Faransa.
An dai gudanar da zanga-zangar ne a gaban ofishoshin jakadancin kasar Chadi, da na Amurka da Faransa har da babban ofishin kugiyar kasashen Afirka ta ECOWAS.
Idan za’a iya tunawa, tun a shekarar 1991 tsohon shugaban Kasar ta Chadi Marigayi Idris Debby ke rike da shugabancin kasar.
Bayan rasuwarsa a watan Afrilun wannan shekara, dan sa Mahamat Idriss Déby wanda janar ne na soja ya haye kujerar mulkin kasar.
Saurari cikakken rahoton cikin sauti: