Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Mutane Kimanin 790 Suka Harbu Da Cutar Korona A Najeriya


NCDC COVID-19 PIC
NCDC COVID-19 PIC

Hukumar yaki da cutattuka masu yaduwa ta Najeriya wato NCDC ta bayyana cewa kimanin mutane 790 suka kamu da cutar korona birus a kasar.

Kididdigar hukuma ta bayyana cewa wannan ne adadi mafi yawa da aka samu a cikin watanni 6 na baya-bayan nan.

Alkaluman sun kuma yi nuni da cewa mutum daya ya rasa ransa a bisa kamuwa da cutar kamar yadda hukumar ta bayyana a shafinta na yanar gizo.

A an samu adadin wadanda suka kamu da cutar covid din ne a jihohi 13 bisa rahoton da hukumar NCDC ta fitar ta yanar gizo da safiyar yau Alhamis.

Jihar Legas ce ke kan gaba da adadi mafi yawa na wadanda suka kamu da cutar 574, sai jihar Ribas mutane 83, da kuma jihar Ondo mutane 38.

Sauran jihohin sun hada da Ogun da mutane 31, Oyo 23, Delta 10, Birnin tarayya Abuja 9, Ekiti 7, Edo na da 6, Osun mutane 4, Anambra 2, Bayelsa 2, da kuma jihar Filato da mutum daya.

A halin yanzu dai jumlar wadanda suka kamu da cutar Covid-19 ya kai akalla mutane dubu 179,908 a kasar, inda mutane kimanin dubu 166,203 suka warke, kuma mutane dubu 2,195 suka rasa rayukansu sakamakon kamuwa da cutar a fadin jihohi 36 hade da babban birnin tarayya Abuja.

Alkaluman hukumar lafiya ta duniya sun tabbatar da cewa sama da mutane miliyan 200 suka kamu da cutar a fadin duniya, inda kimanin miliyan 4 suka rasa ransu a sakamakon cutar ta Covid.

An sami barkewar cutar korona bairos kashi na uku ne sakamakon bullar nau’in Delta na cutar, wanda ya yi sandiyyar shugabannin kasashen duniya suka takaita zirga-zirga da kuma jinkirta sake bude ayyukan yau da kullum domin farfado da ayyukan tattalin arzikin da akasari aka rufe a shekarar 2020.

Haka kuma, bullar nau’in na Delta na cutar ya kawo cikas ga aikin bada allurar rigakafin cutar a duniya.

XS
SM
MD
LG