Farashin kayan masarufi na ‘kara hawa a kudu maso gabashin Najeriya, yayin da musulmi ke azumin watan Ramadan.
Kwamitin raya yankin arewa maso gabas na bukatar Naira Tiriliyan biyu cikin shekaru goma, don aikin raya yankin arewa maso gabas da hakan zai baiwa dukkan wadanda suka rasa muhallansu damar komawa garuruwansu na asali.
Ciki da Gaskiya Wuka Bata Hudashi
Wani abin fashewa ya fashe a wata kasuwa dake birnin kasuwanci na Aba dake jihar Abia, inda mutane da dama sun jikkata.
A dai dai lokacin da ake ci gaba da cece-kuce game da zabukan shugabanin jam’iyar APC a matakin jihohi da aka kammala a jiya asabar, yanzu haka hukumar zabe, INEC a jihar Adamawa tace bangare guda kawai ta sani, kuma da ita zata yi aiki.
An tabbatar samun wadansu mutane uku dauke da kwayar cutar Ebola a Damokaradiyar Jamhuriyar Congo, bisa ga cewar ministan lafiya na kasar.
Hukumar tsaron farin kaya ta Civil Defense a jihar Nasarawa ta yi nasarar cafke wasu mutane dake tafka manyan laifuka, ciki har da wasu da bindigogi a yankin karamar hukumar Toto da ake rikici.
Majalisar tattalin arziki karkashin jagorancin mataimakin shugaban kasa Farfesa Yemi Osinbajo, ta yi wani babban taronta a Abuja inda ta bankado wata badakala da ta shafi wasu kamfanonin gwamnatin tarayya.
Rahotanni dai sun bayyana cewa yanzu haka al’ummomin kauyukan Wadukun da Kwoh zuwa bangaren Tigno dake karamar hukumar Lamurde, cikin jihar Adamawan na cikin zaman dar-dar lamarin da yasa wasu mazauna yankunan kauracewa gidajensu.
Yayin da ake haramar fara azumin watan Ramadan a jihohin Adamawa da Taraba an tsaurara matakan tsaro don kare rayuka.
Rundunar sojojin ruwan Najeriya sun gudanar da sintirin awa 22,000 cikin shirin samar da tsaro a kasar ta cikin ruwa.
Noma Tushen Arziki
Wata kungiyar al’ummar ‘yan arewacin Najeriya dake zaune a kudancin kasar ta gudanar da taron zaman lafiya tare da nuna rashin jin dadi game da tabarbarewar tsaro a kasa baki daya.
Wata budurwa ta rasa ranta a wajen zaben kananan hukumomi a jihar Oyo.
Hedikwatar tsaron Najeriya ta yi karin haske kan atisayen Tseren Bera da ta gudanar don wanzar da zaman lafiya a jihohin Benue da Taraba.
Yau ranar 12 ga watan Mayu ake bikin tunawa da ma’aikatan jinya a fadin duniya.
Babban sakataren kungiyar hadin kan Krista ta Najeriya CAN, Rev Dakta Musa Asake ya rasu ranar Juma’a.
Domin Kari