Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Nasarar Da Sojojin Najeriya Suka Samu a Atisayen Ayem Akpatuma


Sojojin Najeriya.
Sojojin Najeriya.

Hedikwatar tsaron Najeriya ta yi karin haske kan atisayen Tseren Bera da ta gudanar don wanzar da zaman lafiya a jihohin Benue da Taraba.

A cewar kakakin rundunar tsaron Najeriya Janar John Agim, a jihohin Benue da Taraba sun cafke kimanin ‘yan bindiga 183, an kuma kama wasu ‘yan kungiyoyin matsafa ‘barayin shanu da sauran bata gari fiye da 100 a jihohin biyu.

Itama rundunar sojin Najeriya ta daya mai hedikwata a birnin Kaduna ta kama wasu ‘yan bindiga a wasu yankunan dake karkashin ikonta kuma tuni an mikasu ga hannun rundunar ‘yan sandan Najeriya don taukar mataki na gaba.

Kakakin John Agim, ya kara da cewa an sami bindigogi da harsasai yayin wannna atisaye na Ayem Akpatuma a jihohin Benue da Taraba.

Kasancewar sojojin a jihohin biyu ya ‘karawa jama’a kwarin gwiwa musamman a kauyuka da sansanonin ‘yan gudun hijira, wadanda rikice-rikicen ya raba su da gidajensu, sannan hakan ya hanawa ‘yan bindiga damar kai hare-hare.

Amma duk da nasarorin da rundunar tsaron ta samu masanin tsaro mallam Kabiru Adamu, ya ce karfin soja kadai ba zai magance matsalar baki daya ba, kasancewar su sojoji an basu horo ne wajen yin amfani da karfi don dakile matsala, wanda hakan zai kwantar da matsalar cikin gida ne kawai.

Domin cikakken bayani saurari rahotan Hassan Maina Kaina.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:24 0:00

Facebook Forum

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG