Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Zaben Shugabannin Jihohi Na APC Ya Bar Baya Da ‘Kura a Adamawa


ADAMAWA: Sakatariyar APC ta jiha
ADAMAWA: Sakatariyar APC ta jiha

A dai dai lokacin da ake ci gaba da cece-kuce game da zabukan shugabanin jam’iyar APC a matakin jihohi da aka kammala a jiya asabar, yanzu haka hukumar zabe, INEC a jihar Adamawa tace bangare guda kawai ta sani, kuma da ita zata yi aiki.

Zaben shugabanin jihohin na jam’iyar APC dake mulki a Najeriya, ya bar baya da ‘kura inda kamar sauran wasu jihohi, a jihar Adamawa ma bangarori biyu ne suka gudanar da zaben, wato ‘yan bangaren tsohon gwamnan jihar Murtala Nyako da suke tare da su tsohon sakataren gwamnatin tarayya, Babachur David Lawal, da Nuhu Ribadu da wasu kusoshin jam’iyar, da kuma yan bangaren gwamnan jihar Senata Muhammadu Bindow Umaru Jibrilla dake marawa shugabanin dake kan karaga.

Bayan kammala zabukan biyu dukkanin bangarorin sun fitar da shugabanin da suka zaba, batun da yanzu ya raba kawunan ‘ya ‘yan jam’iyar a jihar, koda yake kwamishinan hukumar zabe a jihar Barista Kassim Gana Gaidam, ya ce bangare guda suka sani wato yan bangaren gwamna.

To ko me yan daya bangaren ke cewa ne game da wannan zabe? Hon. Baba Oga shine sabon sakataren wannan bangaren, ya ce su kam suna nan daram.

Hon. Dimas Ezra shi aka zaba a matsayin sabon shugaban jam’iyar APC, na bangaren su Murtala Nyako, yayin da shi kuwa shugaban riko na jam’iyar Ibrahim Bilal ya yi tazarce a bangaren gwamna, wanda kuma lokaci ne kawai ke iya tabbatar da yadda zata kaya.

Domin karin bayani saurari cikakken rahotan Ibrahim Abdul’aziz.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:43 0:00

Facebook Forum

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG