Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Farashin Kayayyaki Sun Tashi a Yankin Kudu Maso Gabas


Kayayyakin Masarufi
Kayayyakin Masarufi

Farashin kayan masarufi na ‘kara hawa a kudu maso gabashin Najeriya, yayin da musulmi ke azumin watan Ramadan.

Muryar Amurka ta zanta da wasu kananan ‘yan kasuwa da wasu magidanta a yankin kudu maso gabashin Najeriya. A cewar Mallam Mika’ilu Yaro wani karamin dan kasuwa, shigowar azumi yasa kayan masarufi sunyi tsada, da suka hada da Tumatir da Albasa da Attarihu, kuma gashi yanayin kasuwa babu kudi.

Itama wata ‘yar kasuwa mai suna Usilia Okeke, cewa ta yi lokacin da aka fara azumi farashin kayayyakin da suke sayarwa ya tashi, har ma ya ribanya kudin da suke sarowa a baya.

Alhaji Tijjani Umaru daga kasuwar Abakaliki, cewa duk wasu kayayakin masarufi da suke saya suna sayarwa a kasuwa farashinsu ya karu.

Sai dai mallam Rabi’u Isufu Bagobiri wani mai shago a tsohon garken garin Okigwe dake jihar Imo, ya ce har yanzu farashin wasu kayan marmari na nan a yadda suke basu canza ba.

Masu sharshi kan al’amura na ganin tashin farashin kayayyaki lokacin azumi yana da nasaba da rashin Imani da son zuciya, kasancewar wasu mutane na jiran samun dama irin ta wannan watan domin su kara kudin kayayyakinsu don neman riba mai yawa.

Domin karin bayani saurari rahotan Alphonsus Okoroigwe.

please wait

No media source currently available

0:00 0:04:36 0:00

Facebook Forum

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG