Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Gano Wata Sabuwar Badakala Daga Wasu Kamfanonin Gwamnatin Tarayya


ABUJA: NNPC
ABUJA: NNPC

Majalisar tattalin arziki karkashin jagorancin mataimakin shugaban kasa Farfesa Yemi Osinbajo, ta yi wani babban taronta a Abuja inda ta bankado wata badakala da ta shafi wasu kamfanonin gwamnatin tarayya.

Majalisar ta bankado cewa akwai kamfanoni gwamnatin tarayya akalla guda 17 da basu tura kudade na shekara-shekara da ake bai wa gwamnatin tarayyar Najeriya, da yawan kudaden ya wuce hankali.

Bayan da majalisar ta kammala taron gwamnan jihar Zamfara, Abdul'aziz Abubakar Yari, ya ce idan Allah kaimu wata mai zuwa za a fara yin aiki da rahotan, kuma an sake sawa a zakulo mutanen da ke da hannu a badakalar, domin gurfanar da su gaban kotu.

Kwararre mai fashin baki kan tattalin arziki Shu’aibu Idris, ya bayyana cewa lalle akwai babbar badakala dake tattare da irin wannan tsarin, gwamnatocin jihohi da na kananan hukumomi sune gaba-gaba a wajen cutuwa.

Domin karin bayani saurari rahotan Umar Faruk Musa

please wait

No media source currently available

0:00 0:04:03 0:00

Facebook Forum

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG