Taron kungiyar ‘yan Arewacin Najeriya don tabbatar da zaman lafiya a kudancin Najeriya, an shirya shi ne a dai dai lokacin da ake samun tashe-tashen hankula a yankunan Arewacin Najeriya.
Lamarin da ‘yan Arewa mazauna kudancin kasar ke bayyana rashin jin dadinsu game da afkuwar rikici a yankin, inda kuma suke kira ga mahukunta na kudanci da ma Arewacin kasar da gwamnatin tarayya da su tashi tsaye wajen magance al’amura dake ci gaba da saka kasar cikin halin rashin tsaro.
Alhaji Ibrahim Dinar, dake zama ‘daya daga cikin shugabannin kungiyar, ya ce manufar kungiyar shine kawo gyara ga duk al’amuran da ke damunsu da kuma ‘kasa baki ‘daya.
An dai kafa wannan kungiya ne domin yadda ake muzgunawa wasu ‘yan kasuwa dake zaune a kudu, ta hanyar kamasu a daure ba tare da aikata wani laifi ba, inda kungiyar ke zuwa tana kwatowa duk wadanda aka kama hakkinsu.
Domin karin bayani saurari rahotan Babangida Jibrin daga Lagos.
Facebook Forum