Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Zaben Kananan Hukumomi a Jihar Oyo


Tambarin hukumar zaben Najeriya.
Tambarin hukumar zaben Najeriya.

Wata budurwa ta rasa ranta a wajen zaben kananan hukumomi a jihar Oyo.

Ranar Asabar aka gudanar da zaben kananan hukumomi a jihar Oyo, inda aka fitar da rahoton wata budurwa mai suna Kofo ta rasa ranta a unguwar Idi Oro dake yankin Queens Cinema a Ibadan.

Kisan budurwar yayi sanadiyar haddasa zanga-zanga.

Gwamnan jihar Oyo, Sanata Abiola Ajimobi, ya yabawa jama’ar jihar game da gudanar da zaben lafiya kuma sahihi.

Shima shugaba hukumar zabe ta jihar Oyo, Jide Ajeigbe, ya tabbatar da cewa an gudanar da zaben cikin kwanciyar hankali, kuma ya bukaci ‘yan takarar da su karbi sakamakon zaben.

Sai dai jam’iyyun adawa sun ki shiga zaben da aka gudanar.

Domin karin bayani saurari rahotan Hassam Umaru Tambuwal.

please wait

No media source currently available

0:00 0:01:28 0:00

Facebook Forum

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG