Hadakar kungiyar makiyayan Najeriya ta maida martani game da kisan da sojoji suka yiwa wasu Fulani makiyaya sama da goma a yankin Katibu, dake karamar hukumar Lau a jihar Taraba.
A karo na uku, babban sufeton ‘yan sandan Najeriya, Ibrahim Idris ya ki amsa goron gayyatar da Majalisar Dattawa ta yi masa.
Biyo bayan yawaitar makamai a hannun jama’a ba bisa ka’ida ba, Majalisar Dattawan Najeriya ta gayyaci shugabannin rundunonin tsaron kasar su bayyana gabanta.
Noma Tushen Arziki
Ciki da Gaskiya Wuka Bata Hudashi
Rundunar sojojin saman Najeriya na bukin cika shekaru 54 da kafuwa, tare da duba ire-iren nasarorin da rundunar ta cimma cikin wadannan shekarun.
Wasu matasan jam’iyyar APC sun kona wani bangare na sakatariyar kamar hukumar Ningi, a jihar Bauchi.
Ya yin da Najeriya ta kulla yarjejeniyar cinikayya da babban kamfanin kera jiragen sama na Amurka mai suna Boeing, don sake kafa sabon kamfanin jiragen sama na kasa, yanzu haka an dauki matakin gyara harkokin sufuri a kasar.
Wata babbar kotu a jihar Kogi ta bayar da umarnin a mayar da Sanata Dino Malaye babban asibitin Abuja domin a ci gaba da kula da lafiyarsa, kamar yadda jaridar Daily Trust ta rawaito.
Amurka ta yi Allah wadai da harin kunar bakin wake da aka kai garin Mubi, dake jihar Adamawa.
Babban bankin Najeriya CBN da na kasar China sun shiga yarjejeniyar musayar kudin kasashen biyu, don saukaka huldar kasuwanci ba tare da neman dalar Amurka ba.
Shugaban Najeriya Mohammadu Buhari ya ce bai gamsu da cewa matakin barin jihohi su kafa rundunar ‘yan sandansu shi ne zai kawo karshen tashe-tashen hankula a kasar.
Gwamnatin Najeriya ta hana shigowa ko sarrafa duk wani ruwan maganin hana tari dake ‘dauke da sinadarin Codeine.
Yayin da alkaluman mutanen da suka mutu a tagwayen harin kunar bakin wake da aka kai garin Mubi ke karuwa, yanzu haka an garzaya da wadanda ke da munanan raunuka zuwa cibiyar lafiya dake fadar jihar wato FMC Yola.
Shugaban Najeriya Mohammadu Buhari na shirin ganawa da shugaban Amurka Donald Trump gobe Litinin a birnin Washington DC.
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari na kan hanyarsa ta zuwa Amurka domin amsa gayyatar takwaransa shugaba Donald Trump.
Ranar Asabar idan Allah ya kaimu shugaban Najeriya Mohammadu Buhari zai amsa goron gayyatar shugaban Amurka Donald Trump, inda zai kai wata gajeriyar ziyarar aiki.
Domin Kari