Hukumar kula da lafiya na matakin farko a jihar Neja ta koka da rashin samun kudaden tafiyar da aikace-aikacen hukumar daga kananan hukumomi.
Kula da lafiyar mutanen karkara na daya daga cikin muhimman bukatu da al’umma ke matukar bukata ga hukumomi a kowanne bangare na duniya.
Hakan yasa a Najeriya aka samar da hukumar kula da lafiya matakin farko da ke samun kulawa daga gwamnatin tarayya da na jihohi da kuma kananan hukumomi, wadanda baki ‘dayansu ke bayar da wani kaso na kudaden tafiyar da hukumar.
A jihar Neja dai, bayanai na nuna cewa hukumar ba ta samun kasonta daga kananan hukumomi 25 na jihar, al’amarin da ke kawo cikas wajen aikin kula da lafiyar mata masu juna biyu, da kuma kananan yara a yankunan karkara.
Domin karin bayani saurari rahotan Mustapha Nasiru Batsari.
Facebook Forum