Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Mutane Da Yawa Ne Suka Raunata Bayan Fashewar Wani Abu a Birnin Aba


Wani abin fashewa ya fashe a wata kasuwa dake birnin kasuwanci na Aba dake jihar Abia, inda mutane da dama sun jikkata.

Fashewar wani abu mai kama da bam daga cikin kekunan a daidaita sahu cikin dandazon jama’a a birnin kasuwanci na Aba a jihar Abia.

Lamarin dai ya faru ne a kasuwar ‘yan doya dake garin Aba, inda fashewar ta yi sanadiyar raunata mutane masu yawa duk da yake ba a sami asarar rayuka ba.

Muryar Amurka ta samu zantawa da wasu mutanen da fashewar ta shafa, inda wasu suka bayyana cewar sakamakon fashewar wasu karafuna sun warwatsu suka shiga jikin mutanen dake kusa da gurin, lamarin da ya kai sai da aka yiwa wasu aikin tiyatar cire karafan daga jikinsu.

Duk da yake dai Muryar Amurka ta yi kokarin jin ta bakin kwamishinan ‘yan sandan jihar Abia, amma abin ya ci tura, ya zuwa yanzu dai babu wani ko wata kungiya da ta fito ta dauki alhakin harin.

Haka kuma jihar Rivers wasu yan Bindiga sun bude wuta kan wani taron sarakuna a garin okirka, inda aka samu asarar ran wani basarake ‘dan arewacin Najeriya mai suna Abubakar Wurno.

Domin karin bayani saurari rahotan Lamido Abubakar.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:32 0:00

Facebook Forum

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG