Wasu ‘yan siyasa daga Arewaci da Kudancin Najeriya sun kafa gwamnati ko kungiyar sa ido kan ayyukan gwamnati mai ci da su ke zayyanawa da cewa ta gaza.
Cibiyar ba da lasisin kwarewa kan ayyukan kwangiloli ta Najeriya “Chartered institute” ta ce za ta fara daukar matakan gurfanar da wadanda ba su da lasisi a jami’an da kan gudanar da ayyukan kwangiloli don yaki da baragurbi.
Masana tattalin arziki a Najeriya da ma jami’an gwamnati na duba yanda rabon arzikin kasa zai iya amfani har mutane su shaida sun gani a kasa.
Akalla wakilai 3,600 suke halartar babban taron, wanda za a gudanar a ranakun Asabar da Lahadi a Abuja.
Yayin da gwamnati ke cewa dakarun tsaro na birkita lissafin miyagun iri, jama’a na cewa miyagun na sauya dabarar hallaka jama’a ne da mallake dukiyarsu.
A jumma'ar nan Najeriya ke cika shekaru 61 da samun 'yanci daga Burtaniya daga lissafin karbar 'yancin a ranar daya ga watan Oktoba na 1960.
Dalar Amurka na cigaba da tashin gauron zabi a Najeriya duk da barazanar cafke shugaban dandalin bayanan farashin canji na Aboki FX da gwamnan babban bankin Najeriya ya yi.
Babban Shehun darikar Tijjaniyya a Najeriya Dahiru Usman Bauchi ya ce ba su yarda wasu su dau doka a hannu ta hanyar ramuwar gayya bisa kisan gilla ga mabiyansa ba a Jos, wadanda suke komawa jihohinsu bayan ziyarar da su ka kai masa a Bauchi.
Shugaban na magana ne bayan samun rahoton da ke nuna kashi 2.5% na fadin kasar Najeriya a ke amfana da ita wajen aikin noma.
Hukumar alhazan Najeriya NAHCON ta bayyana bankado wasu kamfanonin dillalan aikin hajji da karbar kudi suna nuna cewa za su kai alhazai don gudanar da aikin hajjin bana.
Hukumomin tashoshin teku na wasu kasashen Afirka ta yamma sun daura damarar yaki da barayin teku da ke barazana ga lamuran kasuwancin teku a yankin.
Ma'abota lamuran zabe da siyasa na cewa dawo da hakkin gudanar da zaben fidda gwani hannun hukumar zabe ne zai gyara harkar dimokradiyya a Najeriya.
Tsawon yajin aikin ma'aikatan sashen shari'a a Najeriya ya kawo koma baya ga lamuran adalci don yadda rashin zaman kotuna ya bar wadanda a ke tuhuma da dama a gidajen yari ko ofisoshin 'yan sanda.
An kada kuri'ar dawowa daga rakiyar gwamnatin Buhari yayin da mutane kuma su ka gwale Sanata Sa'idu Dansadau da ya yi wuf ya amshe bututun magana daga Imam Ibrahim Auwal Usama.
Shugaban gungun barayin da su ka sace daliban jami'ar Greenfield a Kaduna Sani Idris Jalingo da a ka fi sani da "Baleri" ya yi barazanar hallaka sauran daliban matukar ba a turo Naira miliyan 100 da baburan Boko Haram 10 ba.
Rahotanni daga jihar Kaduna da ke arewa maso yammacin Najeriya na cewa, an sake sako wani rukunin dalibai biyar daga cikin 'yan makarantar kwalejin horar da ilimin gandun daji da aka sace a watan jiya.
Domin Kari