Tun fara yajin aikin ma'aikatan a farkon watan Afrilu, a ke tattaunawa da sashen zartarwa amma ba a samu bakin zaren ba.
Tasirin yajin aikin ga tafiyar da lamura na kasa baki daya, ya sa babban Alkali Justice Muhammad Tanko kira ga ma'aikatan su dawo aiki duk da baya son sa baki ga lamuran gwamnoni don kada hakan ya zama neman alfarma daga sashen shari'a.
Ma'aikatan sashen shari'ar sun shiga yajin aikin don tilasta gwamnatin tarayya da gwamnoni su bi hukuncin kotu na samun 'yancin gashin kan kudin sashen shari'a.
Karin bayani akan: Muhammad Tanko, jihar Gombe, zanga-zanga, Nigeria, da Najeriya.
Kwamishinan shari'a na jihar Gombe Barrista Zubairu Ciroma na fatar samun sulhu don yadda rashin zaman kotunan ke take 'yancin masu bin shari'a.
Yajin aikin ya sanya lauyoyi yin zanga-zanga zuwa majalisar dokokin Najeriya don neman su sa baki wajen tilastawa sashen zartarwa ya sakewa shari'a mara; inda da alamu sashen zartarwa ba ya sha'awar sakewa alkalai 'yanci 100% don gudun fadawa tsaka mai wuya ba tare da damar rike linzami ba.
Saurari cikakken rahoton cikin sauti: