Damuwar ta shafi yadda a kan samu barayin teku musamman a mashigar teku ta Guinea.
A ziyarar hadin gwiwar kasuwancin teku, tawagar hukumar kasuwancin teku ta Ghana ta kai ziyara Abuja inda ta gana da hukumar sufurin jiragen ruwa ta Najeriya don daukar karin matakan cin riba 100% daga kasuwancin teku.
"Fashi a mashigar tekun Guinea babban kalubale ne, mu a Ghana zan iya cewa mu a da salama a sufuri ta tekunmu, amma in gemun makwabcin ka ya kama da wuta sai ka shafawa na ka ruwa" inji shugabar hukumar kasuwanci ta teku ta Ghana Mrs. Benonita Bismack.
Ta ci gaba da cewa, su na aiki tare da makwabta da jami'an tsaro don tabbatar da tsaron teku a yankin, amma abin takaici mun ji labarin cewa an kai wa wasu jirage hari da sace wasu 'yan kaashen ketare."
A jawabinsa, shugaban hukumar kasuwanci ta jiragen ruwa na Najeriya Mallam Hassan Bello ya ba da tabbacin ingancin matakan da a ka dauka na yaki da 'yan fashin.
Hassan Bello ya koka ga yadda a ke samun jinkirin fiton kaya a tashar teku ta Najeriya amma ya ce hukumarsa ta bullo da wata dabara.
Karin bayani akan: Hassan Bello, Guinea, Ghana, Afirka, Nigeria, da Najeriya.
Najeriya na da tasiri wajen lamuran kasuwanci a yankin Afirka ta yamma da kan sa duk matakan da ta kan dauka na dakatar da shigo da wasu hajoji kan shafi sauran kasashe da ke makwabtaka, har ya kai ga amfani da hanyoyin diflomasiyya wajen daidaita lamura.
Masana tattalin arziki na cewa dogara da Najeriya ke yi wajen shigo da duk muhimman kayan da ta ke bukata daga ketare ciki kuwa har da man fetur na kawo kuncin tattalin arziki da tsadar kayan masarufi.
Saurari cikakken rahoton a cikin sauti: